Hare-hare biyu waɗanda aka kai a cikin kwanaki kaɗan sun yi sanadin mutuwar mutane 30 a garuruwa biyu makwabta da ke jihar Benue a tsakiyar Nijeriya, wacce ta dade tana fama da rikicin kabilanci, in ji wasu majiyoyi.
Yan bindiga sun kashe aƙalla 'yan kasuwa 13 a yammacin ranar Juma'a a Anwase, wani ƙauye a yankin Kwande, in ji jami'in ƙaramar hukuma Ibi Andrew.
Ya ce maharan sun farmaki kasuwar “suka buɗe wuta a kan mutane ba tare da zaɓi ba”.
“Harbin ya bar 'yan kasuwa da mazauna cikin tashin hankali, an lalata kadarori kuma iyalai na neman 'yan uwansu da suka ɓace.”
A ranar Talata, wasu maharan ɗauke da makamai sun kai hari a kasuwar Mbaikyor da ke kusa, inda suka kashe mutane 17, ciki har da wani jami'in ɗansanda, a cewar mazauna biyu na ƙauyen.
Yankin ya sha fama da karuwar tashin hankali a 'yan watannin da suka gabata tsakanin makiyaya Fulani da al'ummomin manoma game da iko da ƙasa da sauran albarkatu.
Duk da cewa ana yawan gabatar da rikicin a matsayin rikicin al'umma, asalin tashin hankalin ya samo asali ne daga rikice-rikicen da suka fi zurfi: takaddamar filaye da ta ƙara tsananta saboda canjin yanayi, yawaitar makamai kanana, da rashin wani nagartaccen martani mai ɗorewa daga gwamnatin Nijeriya.













