Ƙungiyar Turkawa Mazauna Ƙasashen Waje YTB ta saki Littafin Afirka na shekarar 2024, wanda shi ne na baya bayan nan a cikin jerin waɗanda take bugawa shekara-shekara inda take duba irin ci gaban da ake samu a faɗin nahiyar ta Afirka.
A cewar wani bayani daga YTB, Littafin Shekarar Afirka na 2024 shi ne littafin da cikakkun abubuwa da Turkiyya ta tattaro a kan Afirka, inda yake bayani dalla-dalla kan siyasa da tattalin arziƙi da soji da fasaha da muhalli da kuma ci gaban al’umma.
An fara wallafa littafin a 2022 kuma ana samun sa a cikin harshen Turkanci da Ingilishi, inda yake bayani kan manufofi masu kyau a nahiyar, daga ciki har da nasarorin da aka samu kan ilimi da al’adu da fasaha da wasanni da sinima da kaɗe-kaɗe.
Tasirin duniya
Littafin ya kuma tabo abubuwan da suka yi tasiri a fadin duniya, misali sulhun da aka cimma tsakanin Somaliya da Habasha ta hanyar shiga tsakani da Turkiyya ta yi a 2024 da kuma ƙarar da aka shigar kan kisan kiyashi da Jamhuriyar Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra'ila, a cikin labarai daban-daban.
Gabaɗaya littafin ya ƙunshi labarai na hukumomi guda 12 da gudunmawar marubuta 53, wanda ke haifar da jimillar labarai 66 da kuma bita littattafai 9.
Littafin ya buɗe ne da gabatarwa wadda Emine Erdoğan, uwargidan shugaban ƙasa ta Turkiyya, ta rubuta.
Masu ba da gudummawa sun haɗa manyan hukumomin ƙasa kamar Ma'aikatar Harkokin Waje, Ma'aikatar Tsaron Kasa, Hukumar Harkokin Addini (Diyanet), Cibiyar Yunus Emre (YEE), Hukumar Hadin Gwiwa da Daidaitawa ta Turkiyya (TİKA), Gidauniyar Maarif, Hukumar Red Crescent ta Turkiyya (Kızılay), Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu (AA), Kamfanin Rediyo da Talabijin na Turkiyya (TRT), Kwamitin Huldar Tattalin Arzikin Waje (DEİK) da Kamfanin Jiragen Sama na Turkiyya.
Baya ga nazarin fannoni na musamman, wallafar tayi duba kan manyan al'amuran duniya da ke da tasiri ga Afirka — ciki har da rawar da Turkiyya ta taka a shiga tsakani wadda ta taimaka wurin warware rikicin Somaliya da Habasha a 2024 da kuma ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar da Isra’ila kan kisan kiyashi.


















