Trump ya yi barazanar ‘ɗaukar tsattsauran mataki’ idan Iran ta rataye masu zanga-zanga
Iran ta ce 'wasan kwaikwayon' da Washington ke yi zai sake yin rashin nasara.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗin cewa zai ɗauki mataki mai tsauri da ba a fayyace ba muddin hukumomin Iran suka ci gaba da barazanar rataye wasu masu zanga-zanga, inda Tehran ta kira gargaɗin Amurka a matsayin "share fagen kai hari na soji".
Trump - wanda a baya ya shaida wa masu zanga-zanga a Iran cewa "taimako yana nan zuwa" - ya ce a ranar Talata a wata hira da CBS News cewa Amurka za ta ɗauki mataki idan Iran ta fara rataye masu zanga-zanga.
Masu gabatar da ƙara na Tehran sun ce hukumomin Iran za su gurfanar da wasu mutane a gaban ƙuliya bisa zargin "moharebah", ko "yaƙi da Allah", kan wasu da ake zargi da hannu a zanga-zangar da ake yi a ƙasar.
"Za mu ɗauki mataki mai ƙarfi idan suka yi irin wannan abu (suka rataye masu zanga-zanga)," in ji shugaban Amurka, wanda ya yi ta maimaita barazanar kai wa Iran hari da ƙarfin soji.
"Lokacin da suka fara kashe dubban mutane - kuma yanzu kana gaya min game da ratayewa. Za mu ga yadda hakan zai yiwu," in ji Trump.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka a shafinta na X na harshen Farisanci ta ce an yanke wa Erfan Soltani mai shekaru 26 hukuncin kisa kuma za a zartar da hukuncin ranar Laraba.
"Erfan shi ne mai zanga-zanga na farko da aka yanke masa hukuncin kisa, amma ba zai zama na ƙarshe ba," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen, inda ta ƙara da cewa an kama 'yan Iran fiye da 10,600.
A halin yanzu, ofishin Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya ya wallafa wata sanarwa a X, yana mai alƙawarin cewa "wasan kwaikwayo" na Washington zai "sake yin rashin nasara".
"Mafarkin Amurka da manufofinta game da Iran sun samo asali ne daga sauye-sauyen gwamnati, tare da takunkumi, barazana, tashin hankali da aka ƙirƙira, da hargitsi waɗanda ke aiki a matsayin hanyar da za a bi don samar da hujjar kai harin soja," in ji saƙon da aka watsa.
Kafafen watsa labarai na gwamnatin Iran sun ce an kashe gomman jami'an tsaron ƙasar, inda jana'izarsu ta koma manyan tarurrukan goyon bayan gwamnati.
Mahukuntan Tehran sun sanar da taron jana'izar jama'a a babban birnin ranar Laraba don "shahidai" da aka kashe a kwanakin baya bayan nan.
Kungiyoyin kare haƙƙin dan adam suna zargin gwamnati da harbin masu zanga-zanga da kuma ɓoye girman matakin da aka ɗauka tare da toshe intanet wanda yanzu ya wuce kwanaki biyar.
Hukumomin Iran sun dage cewa sun sake samun iko a ƙasar bayan dararen zanga-zangar gama gari a duk faɗin ƙasar.