| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Rikicin Nijeriya ya tilasta wa dubban mutane tserewa zuwa Nijar: Majalisar Ɗinkin Duniya
UNHCR ta ce kwararar waɗannan mutane na ƙara matsin lamba kan albarkatun Nijar, wadda tuni take ɗauke da ’yan gudun hijira da masu neman mafaka sama da 500,000, ciki har da kusan ’yan Nijeriya 327,500.
Rikicin Nijeriya ya tilasta wa dubban mutane tserewa zuwa Nijar: Majalisar Ɗinkin Duniya
Rikicin Nijeriya ya tilasta wa dubban mutane tserewa zuwa Nijar: Majalisar Ɗinkin Duniya

Kusan mutum 64,000 ne suka tsere daga arewacin Nijeriya zuwa makwabciyarta Nijar a bana, domin guje wa hare-haren ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, kamar yadda hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.

Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta ce kwararar waɗannan mutane na ƙara matsin lamba kan albarkatun Nijar, wadda tuni take ɗauke da ’yan gudun hijira da masu neman mafaka sama da 500,000, ciki har da kusan ’yan Nijeriya 327,500.

Haka kuma, wasu ’yan Nijeriya ɗaruruwa sun nemi mafaka a Benin.

Mafi yawan waɗanda suka isa kwanan nan sun zauna ne a yankunan Diffa da Tahoua da ke kan iyakar ƙasar. UNHCR ta ce mutum sama da 23,000, waɗanda fiye da kashi biyu bisa uku daga cikinsu yara ne, sun isa yankin Diffa shi kaɗai tun farkon wannan shekara.

“Dubban ’yan gudun hijira da suka iso kwanan nan, da dama daga cikinsu yara ne, na fafutukar rayuwa sakamakon ƙarancin abinci, tsaftataccen ruwa, matsuguni da muhimman hidimomi, yayin da tallafin jin ƙai ya yi ƙaranci matuƙa,” in ji kakakin UNHCR, Dominique Hyde, a cikin wata sanarwa ranar Talata.

Matsugunan wucin-gadi

Ta ce iyalai da dama na zaune ne a matsugunan wucin-gadi, yayin da mata kan yi tafiyar kilomita da dama a kowace rana domin samo ruwa.

Yawaitar mutanen da ke tserewa daga gidajensu na nuna irin tasirin da rikicin arewacin Nijeriya ke yi ga sauran ƙasashen yankin. A cikin shekaru goma da suka gabata, hare-haren Boko Haram, ’yan ta’addan Daesh da ƙungiyoyin masu aikata laifuka sun raba miliyoyin mutane da muhallansu.

Ƙungiyoyin agaji sun bayar da rahoton ƙaruwar matsalar tamowa, cututtukan numfashi da ƙarancin tsaftar muhalli a tsakanin waɗanda suka iso kwanan nan.

Haka kuma, damuwar da ta shafi kariyar waɗannan mutane na ƙaruwa. Kashi biyar cikin ɗari kawai na ’yan gudun hijirar da suka isa Nijar a bana ne aka yi wa rajista a hukumance, lamarin da ya sa da dama ba su da takardun da ake buƙata domin samun tallafin jin ƙai da wasu hidimomin gwamnati.

UNHCR na neman dala miliyan 11.4 domin faɗaɗa ayyukan tallafinta a Nijar, Nijeriya da Benin. Hukumar ta yi gargaɗin cewa dubban iyalai da rikici ya raba da muhallansu na iya rasa muhimman tallafe-tallafe idan ba a samu ƙarin kuɗaɗen gudanar da ayyukan agajin ba.