Zaftarewar ƙasa a wani wajen haƙar ma'adinan zinare ba bisa ƙa'ida ba ya yi ajalin aƙalla mutane 100 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a kan iyakar ƙasar da Kamaru.
Har kawo lokacin haɗa wannan rahoto ana ci gaba da gudanar da bincike bayan hatsarin da ya faru a wurin haƙar ma'adinai na Zamboye, kimanin kilomita 50 daga garin Baboua na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a ranar Talata da rana.
Hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna wani ɓangare na ƙasa a babban wurin haƙar ma'adinai, inda ɗaruruwan masu haƙar ma'adinai na hannu ke aiki, suna ballewa suna binne mutane a kan hanyarsu.
Majiyoyi da dama na yankin sun ce kimanin mutane 100 sun mutu, wasu da yawa kuma sun ji rauni.
"Kasa ta zaftare gaba ɗaya ta binne mutane," kamar yadda Cedric Mbango, wani ma'aikacin haƙar ma'adinai a wurin ya shaida wa AFP, yana mai bayyana lamarin a matsayin "mummunan bala'i".
Ana kyautata zaton zaftarewar ƙasa ta faru ne sakamakon "ruftawar wasu ramukan ƙarƙashin ƙasa da masu haƙar ma'adinai ke aiki", in ji mai gabatar da ƙara na Baboua a cikin wata sanarwa, yana mai sanar da buɗe binciken shari'a.
"A wannan matakin yana da wahala mu tantance adadin mutanen da suka mutu," in ji Laurent Ngon Baba, Jami'in da aka zaɓa a Baboua, ya shaida wa AFP da sanyin safiyar Laraba.
Aƙalla mutane huɗu daga cikin waɗanda abin ya shafa 'yan ƙasar Kamaru ne, kamar yadda jaridar Cameroon Tribune ta ruwaito.
An kai waɗanda suka tsira zuwa asibiti a Baboua, yayin da ake ci gaba da binciken a ranar Laraba.
Ana yawan samun zaftarewar ƙasa a wuraren ayyukan da ba bisa ka'ida ba a wasa sassan ƙasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Gregoire Mvongo, Gwamnan Yankin Gabashin Kamaru, ya faɗa wa gidan rediyon CRTV na jama'a cewa suna "aiki tare da abokan aikinmu na Afirka ta Tsakiya don magance abin da ya biyo bayan wannan bala'i".
















