Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai (OPHK), da ke yaƙar ta’addanci a arewa maso gabashin Nijeriya sun kashe fiye da ‘yanta’adda 20 a wurare daban daban a ƙananan hukumomin Monguno da Biu na jihar Borno.
Hedikwatar Operation Haɗin Kai ta ce ɓangaren jiragen yaƙinta ne ya kai samamen bisa amfani da bayanan sirri kan wuraren da ‘yanta’adda suka taru a wurare daban daban a faɗin jihar Borno tsakanin daren 21 zuwa sanyin safiyar 22 ga wtaan Agusta na shekarar 2026.
Ta bayyana cewa hare-haren sama na haɗin giwa da aka yi sun biyo bayan bayanan sirri masu tushe da suka gano tafiya da taruwar waɗanda ake zargi da kasancewa ‘yanta’adda.
Ta bayyana cewa hare-haren sun yi nasarar kassara wuraren da aka gano da kuma katse ƙoƙarin taruwar ‘yanta’addan domin aika-aika a yankin.
“A ɗaya daga cikin samamne, wani jirgin tattara bayanan sirri mai makami ya gano tare da bibiyar wasu da ake zargin ‘yanta’adda ne a yankin Aduwa a ƙaramar hukumar Monguno kafin ya gano ƙarin taron da ya fi yawa a wurin,” kamar yadda rundunar ta bayyana a wata sanarwar da muƙaddashin jami’in watsa labaranta, keftin Mohammed Goni ya fitar.
“Bayan bin ƙa’idojin aiki da suka dace da kuma samun izini, an ƙaddamar da hari mara kuskure kan waɗanda aka gano ɗin. Binciken Bayan Yaƙi da aka yi daga baya ya nuna cewa harin ya samu wani tarin ‘yanta’adda, inda aka kashe kimanin ‘yanta’adda 16 a hare-hare mara kuskure biyu.”
Ta ƙara da cewa jirgin yaƙin ya ci gaba da tattara bayanai a yankin har zuwa lokacin da ya gano wani gungun ‘yanta’adda da ke ƙoƙarin sake taruwa a wani wuri daban daga inda aka fara kai wa hari.
Sanarwar ta ce an sake kai hare-hare mara kuskure inda binciken bayan harin ya nuna cewa an kassara kimanin ‘yanta’adda 10.
A wani samamen na daban kusa da Buratai a ƙaramar hukumar Biu, sanarwar ta ce wani jirgin yaƙin Operation Haɗin Kai ya bi wasu da ake zargin ‘yanta’adda ne a wani wuri a yankin.
“Bayan tattara bayanan sirri na tsawon lokaci da kuma izini da ya dace, jirgin ya kai hari mara kuskure wanda ya afka wa waɗanda aka ganon, inda a kashe ‘yanta’adda 10,” in ji sanarwar.





















