| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Trump ya amince da yarjejeniyar shirin nukiliya na farar-hula da Saudiyya — Rahoto
Shugaban Amurka Donald Trump ya amince da wata muhimmiyar yarjejeniya da Saudiyya wadda za ta samar wa ƙasar wani shirin nukiliya na farar-hula, a cewar rahoton jaridar The Wall Street Journal.
Trump ya amince da yarjejeniyar shirin nukiliya na farar-hula da Saudiyya — Rahoto
Trump ya sa hannu kan wata gagarumar yarjejeniyar nukiliya da Saudiya

Shugaban Amurka Donald Trump ya amince da wata muhimmiyar yarjejeniya da Saudiyya wadda za ta samar wa ƙasar wani shirin nukiliya na farar-hula, a cewar rahoton jaridar The Wall Street Journal.

Da take ambaton jami'an Amurka, jaridar ta ce yarjejeniyar, wadda za ta ɗauki tsawon shekaru 30, an ƙiyasta za a kashe gomman biliyoyin daloli wajen aiwatar da ita.

Kazalika a cewar rahoton, an tsara yarjejeniyar ce don bai wa kamfanonin Amurka damar taka gagarumin rawa wajen bunƙasa albarkatun nukiliya na Saudiyya yayin da kuma ake sa ran za ta fitar da sauran kamfanonin ƙasashen waje daga ƙasar.

Haka kuma, ɗaya daga cikin muhimman matakan da yarjejeniyar ta ƙunsa, sun haɗa da shirye-shiryen kamfanonin Amurka na gina masana'antar tace sinadarin uranium a Saudiyya, wanda za a amince da shi bayan wata bita ta haɗin gwiwa tsakanin Washington da Riyadh.

Rahoton ya ce yarjejeniyar za ta bai wa Amurka rawar da za ta taka wajen sa ido kan kudurin nukiliyar Saudiyya, wanda jami'an gwamnatin Trump suka ce zai iya taimakawa wajen hana amfani da shirin wajen samar da makamai.

Ko da yake, yarjejeniyar, wadda ake sa ran za a aika wa Majalisar Dokokin Amurka don yin nazari a kanta a 'yan kwanaki masu zuwa, akwai yiwuwar ta fuskanci adawa daga 'yan majalisar da ke nuna damuwa game da faɗaɗa karfin nukiliya a Gabas ta Tsakiya.