Nijeriya ta ƙwato kuraye biyu, beguwa da wasu tsuntsaye da ake ba wa kariya a wajen masu fasa-ƙwauri

Hukumar kwastan ta Nijeriya tace a ranar Talata jami’anta sun kama wasu kuraye biyu, beguwa da tsuntsaye 24 da ake ba wa kariya.

By
Nijeriya ta ce jami’anta sun kama wasu kuraye biyu, beguwa da tsuntsaye 24 da ake ba wa kariya a ranar 14 ga Afrilun 2026. / Reuters / Reuters

Hukumar kwastam ta Nijeriya tace a ranar Talata jami’anta sun kama wasu kuraye biyu, beguwa da tsuntsaye 24 da ake ba wa kariya, kwacen dabbobin dawa mafi girma tun bayan da majalisar dokoki ta amince da kudirin doka a watan Oktoban 2025 da har yanzu ba a fara aiwatar da ita ba. An kwace dabobin a jihohin Borno da Yobe na areacin kasar.

Kudirin dokar da ke da manufar yin garambawul ga kare namun daji a Nijeriya d akuma kara tsaurin hukunci, ya samu amincewa daga majalisun kasa guda biyu a karshen shekarar bara, amma har yanzu shugaban kasa bai sanya mata hannu ba.

“Akwai mantuwa a cikin kudirin inda wasu jinsin dabbobi da aka bayyana suna fuskantar hatsari a duniya ba a sanya su a cikin masu fuskantar hatsari a Nijeriya ba,” in ji Terseer Ugbor, masanin doka da ya bayar da gudunmawa wajen shirya kudirin. “Dole ne mu koma mu gyara wannan.”

Ugbor ya ce a yanzu an kammala gyaran kuma ana jiran a sanya wa dokar hannu.

Masu rajin kare namun dawa na matsa lamba kan a sanya wa dokar hannu

Kungiyoyin masu rajin kare namun daji un ce suna matsa lamba don ganin an hanzarta saka wa dokar hannu.

“Sanya wa dokar hannu zai karfafa wa masu bincike, masu gabatar da kara da bangaren shari’a da su kawar ba fataucin namun dawa,” in ji Linus Unah, daraktan Yammacin Afirka na kungiyar kare dabbobin dawa ta Wild Life.

Kudirin dokar zai kusantar da dokar kasa da yarjejeniyar kasa da kasa, fadada yawan dabbobin da ake ba wa kariya tare da kawo hukunci mai tsauri, ciki har da zaman kurkuku da tara mai yawa.

Turn watan Oktoba, Hukumar hana Fasa Kauri ta Nijeriya ta kama hauren giwa a Abuja, pangolin masu rai a arewaci da kudancin kasar, jariran zakuna da na birrai a kusa da iyakar Benin, da kuma na baya-bayan nan dabbobin da aka boye a mota a birnin Maiduguri na arewa maso gabashin kasar, in ji wata sanarwar hukumar ta kwantan.

Abdullahi Maiwada, mai magana da yawun kwastan, ya yi maraba tsauraran dokoki da za su taimaka aiwatar da ayyukan kare dabbobin na dawa da ke fuskantar barazanar karewa.