Tsananin rikici a Kudancin Sudan ya yi ajalin akalla mutane 61, ciki har da yara kanana tara, in ji wata kungiyar ma’aikatan lafiya a ranar Laraba, rikicin da yake wani bangare na yakin da ya afka wa kasar tun 2023.
Kungiyar Sudan Network, wadda ke sanya ido kan yawaitar asara a yakin, ta ce a farkon wannan watan ne fada ya barke tsakanin Mayakan Kungiyar ‘Yantar da Sudan da ‘yan kabilar Otoro a garin Kauda, da ke Kudancin Kordofan.
Shugaban ‘yan tawaye Abdulaziz Al-Hilu, wanda ke jagorantar kungiyar ya hade mayakansa da na RSF, kungiyar da ke yakar sojojin Sudan.
Yakin Sudan da ya shiga shekara ta hudu ya bar sojojin rike da iko da arewaci, gabas da tsakiyar kasar, ciki har da yankunan da ke dauke da tashoshin jiragen ruwa.
Shaida daga wadanda suka tsira
Sanarwar da aka fitar daga kungiyar likitocin ta bayar da bayan shaidu da aka tattara a Kudancin Kordofan, inda wadanda suka tsira suka ce an kashe mata biyar da yara tara a rikicin na makonni biyu.
Mohammed Elsheikh, kakakin kungiyar, ya fada wa AP cewa rashin kyakkawan yanayin sadarwa ya sanya da wahala a iya fayyace cikakken adadin, wanda na iya zama sama da haka saboda ana ci gaba da arangama.
Kungiyar likitocin ta kuma ce mayakan ‘yan tawayen sun kona gidaje da shaguna tare da sace kayayyaki.
Wadanda suka tsira sun ce an kai wa fararen-hula hari ba tare da bambancewa ba.
Kungiyar ta kuma yi gagaɗin cewa a yankin Kauda an samu kai munanan hare-hare kuma babu hanya mai kyau da za a bi domin kwashe fararen-hula.
An kai wa fararen-hula hare-hare
A yankin Dilling, wani gari a Kudancin Kordofan, hari da manyan tankoki daga RSF ya kashe mutane bakwai da jikkata wasu 17, kamar yadda wani asibitin yankin ya bayyana.
Daraktan asibitin Umm Bakhita , Omran Teia ya fada wa AP cewa mayakan sun kai wa fararen-hula hari.
Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyi takwas sun zargi bangarorin Sudan biyu da ke rikici da juna da aikata munanan ayyuka, ciki har da karar da kabilu, kisan kare-dangi da cin zarafin mata da cusguna wa fararen-hula.
Kungiyoyin agaji sun ce adadin na iya fin haka sosai a yayin da ba a iya isa ga yankuna da dama da ake rikici a cikin su a kasar.












