Turkiyya ta ci gaba da riƙe kofin Turai na wasan volleyball na mata, bayana ta doke Italiya, kasar da ke riƙe da kofin duniya da na olimfik. Ranar Lahadi ne tawagar matan Turkiyyar ta doke takwararta da ci 3-2, a wasan ƙarshe da aka yi zagaye 5 a brinin Istanbul.
Italiya ta fara wasan da rinjaye, inda zagayen farko-farko da canjaras 6-6, kafin su samu fifikon maki 11-8. Bayan hutun rabin wasa, sun sake cin 14-8, sannan daga baya suka ci 18-9, kafin su ƙarke da ci 25-16.
Sai dai daga bisani, Turkiyya ta harzuƙo, inda Melissa Vargas da Eda Erdem suka jagoranci farfaɗwar har suka rage giɓin zuwa 12-10.
Daga nan sai Turkiyya ta ta daidaita wasan da maki 15-15, sannan ta matsa zuwa 22-20, kuma ta tsaya tsayin-daka ta lashe zagayen gaba da 25-22.
Italiya ta sake samun fifiko a zagaye na uku, inda ta yi fintinkau da maki 8-2. Turkiyya ta rage tazarar zuwa 9-5, amma sai Italiya ta mayar da martani da maki 11-5, sannan daga baya da maki 19-9 kafin ta karɓi ci maki 25-12.
Turkiyya ta taso da ƙarfi a zagaye na huɗu, inda ta ci maki 6-1, sannan ta ƙara zuwa 10-3.
Italiya ta mayar da martani, ta rage giɓin zuwa 14-10 sannan 16-14, amma Turkiyya ta saka karɓe iko a ƙarshe ta ci 25-21, har ta tilasta yin zagaye na biyar don fayyace zakaru, kuma ta lashe gasar.



















