Rundunar juyin-juya-halin Iran (IRGC) ta fara wani atisayen soji a mashigin tekun Hormuz, kwana ɗaya kafin a fara zagaye na biyu na tattaunawa a kaikaice tsakanin ƙasar da Amurka.
Wata sanarwa da ɓangaren hulɗa da jama’a na IRGC ya fitar ranar Litinin ta ce atisayen mai taken “Smart Control of the Strait of Hormuz” an yi shi ne domin tabbatar da shirin dakarun ruwanta.
Ta ce an yi atisayen ne domin tantance shirin tsaro da kuma yanayi na ramuwar gayya na matakin soji a matsayin martani ga barazanar soji a yankin mashigin tekun Hormuz da kuma nuna ƙarfin faɗa-a-ji da Iran take da shi a siyasar yankin.
“Martani na gaggawa, cikakke kuma galaba ta dakaraun IRGC game da makirce-makirce kan tsaro a ɓangaren ruwa shi ne abin da waɗannan dakarun da ke wannan atisayen suka mayar da hankali a kai,” in ji sanarwar.

Mashigin tekun Hormuz, ɗaya daga cikin tsukakkun wurare mafi muhimmanci a duniya da ke tsakiyar mashigin ruwan Oman kuma yana samar da hanyar ruwa ɗaya tilo daga mashigin tekun zuwa cikin teku.
Atisayen na zuwa ne a cikin yanayi na ƙarin ce-ce-ku-ce tsakanin Tehran da Washington, bayan jibge jiragen ruwa masu ɗauke da jiragen yaƙi da jiragen kai hare-haren bam a mashigin tekun Iran
Ranar Juma’a, shugaban Amurka Donald Trump ya ce za a tura wani jirgin ruwa mai ɗauke da jiragen yaƙi zuwa gabas ta Tsakiya.















