| Hausa
DUNIYA
4 minti karatu
Wuta za ku je idan ba ku jefa ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisa ba, in ji Trump ga 'yan Republican
“Kun san abin da zai faru idan ba ku kaɗa ƙuri’a ba? Wuta za ku," in ji Shugaban Amurka Donald Trump a yayin rufe taron Jam’iyyar Republican na zaɓen ‘yan majalisar Amurka da ke tafe a watan Nuwamba.
Wuta za ku je idan ba ku jefa ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisa ba, in ji Trump ga 'yan Republican
"A cikin watanni 19, na cika kowane alkawari da na ɗauka," in ji Trump. / Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga ’yan Jam’iyyar Republican da su kaɗa ƙuri’a a zaɓen ‘yan majalisa da za a yi a watan Nuwamba, inda ya jagoranci magoya bayansa wajen yin alƙawarin fitowa kaɗa ƙuri’a, tare da gargaɗin cewa nasarar ’yan Democrat za ta yi barazana ga manufofin gwamnatinsa.

A yayin rufe taron Jam’iyyar Republican na zaɓen ‘yan majalisar Amurka da ke tafe inda aka gudanar da taron a Dallas da ke Jihar Texas, a daren Alhamis, Trump ya buƙaci mahalarta su maimaita alƙawarin cewa za su kaɗa kuri’a a ranar 3 ga Nuwamba ko kuma a lokacin kaɗa ƙuri’a da wuri, tare da zuwa da abokansu da iyalansu.

“Na yi alƙawari ga shugaban ƙasa mafi girma a tarihin Amurka ... Zan sa abokaina, iyalina, kuma za mu kaɗa kuri’a a ranar 3 ga Nuwamba, ko kuma za mu kada ƙuri’a kafin wannan ranar ... Ban damu da ko an yi mini rajista ko a’a ba.

“Zan yi ƙoƙarin yin maguɗi matuƙa, kamar yadda suke yi,” kamar yadda Trump ya shaida wa taron, yana zargin ’yan Democrat da yin maguɗin zaɓe.

Bayan an kammala alƙawarin, ya ƙara da cewa: “Kun san abin da zai faru idan ba ku kaɗa ƙuri’a ba? Wuta za ku.”

Trump ya yi alƙawarin ci gaba da riƙe ikon Jam’iyyar Republican a Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa, yana ƙalubalantar al’adar tarihi da ke nuna cewa jam’iyyar shugaban ƙasa mai ci kan rasa kujeru a zaɓen tsakiyar wa’adi.

Ya yi gargaɗin cewa idan ’yan Democrat suka sake samun iko, za su “kwace dukiyarku … su lalata masana’antar man fetur da iskar gas ta Texas” tare da “sake ’yantar da masu aikata laifuka su yi fashi, fyaɗe da kisa kamar yadda muka gani shekaru biyu kacal da suka gabata.”

Trump ya jaddada nasarorin gwamnatinsa

A ƙoƙarin ƙara ƙwarin gwiwa ga magoya bayansa, Trump ya yi iƙirarin cewa ya cika dukkan alkawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓensa.

Ya yi nuni da ƙarin darajar hannayen jari a kasuwannin hannayen jari, raguwar farashin magungunan da ake saya da takardar likita, da kuma ƙarin kashe kuɗi kan sojoji, yana mai cewa gwamnatinsa ta mayar da Amurka “ƙasar da ta fi kowace ƙarfi a duniya wajen samar da makamashi da kuma ƙarfin soji.”

Shugaban ƙasar ya kuma jaddada manufofinsa kan shige da fice, yana ambaton kusan kawar da tsallaka kan iyaka ba bisa ƙa’ida ba, tare da yaba wa kansa kan samun amincewar majalisa kan matakan da suka tanadi sabbin rangwamen haraji ga kuɗaɗen aiki bayan lokutan aiki, kuɗaɗen kyauta da ake bai wa ma’aikata, da kuma kuɗaɗen biyan haƙƙoƙin jama’a.

‘Ƙasar ba ta mallakin masu tsattsauran ra’ayi ba ce’

Mataimakin Shugaban ƙasa JD Vance, wanda ya gabatar da babban jawabin dare kafin Trump ya yi magana, shi ma ya yi kira ga ’yan Republican da su kaɗa ƙuri’a domin kare rinjayen jam’iyyar a Majalisa.

“Kada ku miƙa ƙasar ga gungun mahaukata saboda kawai ba ku yarda da mu kan wata manufa ko wata a nan ko can ba,” kamar yadda Vance ya ce.

“Dole ne mu aika da saƙo a wannan watan Nuwamba cewa ƙasar ba ta mallakin masu tsattsauran ra’ayi ba ce. Ba ta mallakin ma’aikatan gwamnati masu bin ƙa’ida kawai ba ce. Ba ta mallakin wanda ya fi kowa kuɗin bayarwa ba ce.”

Vance da Trump ba wai kawai suna ƙara ƙwarin gwiwa ga masu kaɗa ƙuri’a da ke goyon bayansu domin zaɓen tsakiyar wa’adin majalisa na Nuwamba ba ne, har ma suna shirya masu kaɗa ƙuri’arsu domin zaɓen shugaban ƙasa na 2028, wanda ake kallon Vance a matsayin wanda zai gaji Trump bayan ya kammala wa’adinsa na biyu a Fadar White House, kuma dokar wa’adi ta hana shi sake neman wa’adi na uku.