| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeirya sun gano albarusai masu yawa a cikin kwata a Maiduguri
Hukumomi sun ce tuni aka dauki matakin tabbatar da cewa lamarin bai jefe rayuwar jama’a cikin hadari ba, yayin da ake ci gaba da yunƙurin kwashe ruwan da ke cikin kwatar ko za a gano wasu karin makaman.
Sojojin Nijeirya sun gano albarusai masu yawa a cikin kwata a Maiduguri
An gano makaman ne a cikin wata kwata a ungwar Bulumkutu a birnin Maiduguri
3 Janairu 2026

Rundunar sojan Nijeriya ta ce ta gano tulin miyagun albarusai a cikin kwata a unguwar Bulumkutu, a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Wata sanarwa da Jami’in Watsa Labarai na Rundunar Hadin Kai da ke arewa maso gabas Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar da yammacin Asabar ta ce, an samu nasarar gano makaman ne a ranar 2 ga Janairu sakamakon bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu, kuma suka yi aiki da su.

Masu AlakaTRT Afrika - Boko Haram: Ana cin Borno da yaki, in ji Zulum

“Gano makaman ya biyo bayan ci gaba da kasancewa a yankin da dakaru suka yi, bayan killace shi da binciken ƙwaƙwaf da dakarun suka yi, sakamakon samun bayanan sirri, da nufin hana masu aikata laifuka da ‘yanta’adda sakewa su yi ɓarna, musamman ma bayan hallaka ‘yan kunar bakin wake da dama ko kama su a makon jiya,” a cewar Sani Uba.

Ya ce binciken ƙwaƙwaf a yankin ya kai ga gano albarusai 1,270 a cikin wata magudanar ruwa.

Sanarwar ta ce tuni aka ɗauki matakin tabbatar da cewa lamarin bai jefe rayuwar jama’a cikin haɗari ba, “yayin da ake ci gaba da yunƙurin kwashe ruwan da ke cikin kwatar ko za a gano wasu ƙarin makaman.”

Jami’in na soja ya ce an tura dakaru da ƙwararru kan abubuwa masu fashewa daga rundunar ‘yansandan Nijeriya don tabbatar da cewa lamarin bai haifar da wata illa ga jama’a ba.

Rumbun Labarai
Fiye da mutum 50 ne suka mutu a harin 'yan bindiga a jihar Neja ta tsakiyar Nijeriya
‘Yansandan Nijeriya sun gayyaci Fasto Chris Okafor bisa zarge-zargen aikata fyaɗe
Nijeriya ta kama Indiyawa 22 bisa zargin shigar da hodar ibilis ƙasar
Aƙalla mutane 25 sun mutu, an ceto 13 a hatsarin kwale-kwale a Jihar Yobe ta Nijeriya
An kashe fiye da mutum 30, an sace wasu da dama a Jihar Niger a tsakiyar Nijeriya: 'yansanda
Sakon Shugaba Tinubu na Sabuwar Shekara: Za a tallafa wa mutum 1,000 a kowace mazaɓa a Nijeriya
Abin da bincike ya gano na musabbabin annobar cutar ƙoda a Jihar Yobe
Rundunar sojin Nijeriya ta kashe ‘yan ta’adda 47 a farmaki da ta kai a faɗin ƙasar
Gobara ta ƙona Masallacin Shitta-Bey da ke Lagos wanda ke da alaƙa da Daular Usmaniyya ta Turkiyya
Kotu ta ba da umarnin tsare Abubakar Malami da ɗansa a gidan yarin Kuje
Wani abu ya fashe a Babban Asibiti a Jihar Kebbi ta Nijeriya
‘Yan jarida bakwai sun mutu sakamakon hatsarin mota a Gombe
Siyasar Kano: Shin Kwankwaso ne zai tura Gwamna Abba  Jam'iyyar APC ko kuwa gaban kansa yake son yi?
Shugaba Tinubu ya tafi Turai don ci gaba da hutun ƙarshen shekara
Bam da aka binne a titi ya halaka mutane a Jihar Zamfara, wasu da dama sun jikkata
Mun tuntuɓi Turkiyya domin neman agaji kan matsalar tsaro – Shugaban Nijeriya Tinubu
Hare-haren Amurka sun sauka a wuraren da babu 'yan ƙungiyar Daesh a Sokoto, in ji mazauna yankin
Jirgin Saman Sojin Nijeriya C-130 da aka tsare a Burkina Faso ya isa Portugal domin yin gyara
Da haɗin gwiwarmu Amurka ta kai hari Nijeriya: Ma'aikatar Harkokin Waje
Amurka ta kai hari kan mayaƙan Daesh a Nijeriya, in ji Donald Trump