| Hausa
SIYASA
2 minti karatu
Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tsarin aika sakamakon zabe kai-tsaye ta intanet
Tun da fari an samu saɓanin ra'ayi tsakanin Majalisar Wakilai wacce ta yarda a sanya tsarin ya zama dole, da kuma Majalisar Dattawa wacce ta dage kan cewa hakan "zabi ne", ba wajibi ba.
Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tsarin aika sakamakon zabe kai-tsaye ta intanet
Majalisar Dattijai / Nigerian Senate
12 awanni baya

Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tsarin aikawa da sakamakon zabe kai-tsaye ta intanet, wanda ke cikin batun ƙudurin gyaran dokar zaɓe ta shekarar 2022.

Tun da fari an samu saɓanin ra'ayi tsakanin Majalisar Wakilai wacce ta yarda a sanya tsarin ya zama dole, da kuma Majalisar Dattawa wacce ta dage kan cewa hakan "zabi ne", ba wajibi ba.

Majalisar Dattawan ta amince ne bayan wani zaman gaggawa da ta yi a ranar Talata, saboda yadda batun ya tayar da jijiyoyin wuya a ƙasar.

Majalisar Dattijan ta ce aika sakamakon kai-tsaye ta na'ura zai kasance matakin farko na aika sakamakon, amma idan an samu matsalar intanet, INEC za ta yi amfani da rubutawa a takarda wajen aika sakamakon kamar yadda aka saba yi a baya.

Sanata Tahir Munguno ne ya gabatar da ƙudirin a lokacin zaman gaggawa da majalisa ta yi kan dokar, yayin da shugaban majalisar ya Godswill Akpabio ya amince da ƙudirin bayan amincewar sauran ƴanmajalisar.

Majalisar ta kuma kafa kwamiti mai mambobi 12 domin yin aiki da majalisar wakilai don yin nazarin dokokin kamar yadda tsarin amincewa da dokoki ya tanada.

Majalisar ta kira zaman gaggawar ne bayan da ƙungiyoyin fararen-hula da jam'iyyun hamayya suka mamaye harabar majalisar dattawan a ranar Litinin don yin zanga-zangar adawar da ƙin amincewa da majalisar ta yi na wajabta aikata sakamakon zaɓe ta na'ura kai tsaye daga kowace rumfar zaɓe.