Babu zaman lafiya idan Falasɗinawa ba su samu 'yanci ba, in ji Shugaban Afirka ta Kudu Ramaphosa

Shugaban Afirka ta Kudu ya sabunta kiraye-kiraye na dakatar da yaƙin Gaza nan take yayin da yake gargaɗin cewa keta yarjejeniyar tsagaita wuta da ake yi na barazana ga zaman lafiyar yankin da na duniya.

By
Afirka ta Kudu ta nemi a tsagaita wuta nan take da kuma samar da wani tsarin siyasa da zai samar da ƙsar Falasɗinawa mai cin gashin kanta . / Reuters

Zaman lafiya mai adalci da ɗorewa a Gabas Ta Tsakiya ba zai samu ba idan Falasɗinawa ba su samu cikakken ‘yancin tsara makomarsu da ‘yancin ɗan’adam ba, kamar yadda Shugaban Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana ranar Litinin, yana mai gargaɗin cewa keta yarjejeniyar tsagaita wutan da Isra’ila take yi na faɗaɗa rikicin.

Da yake jawabi ga wakilai a taron jam’iyyarsa ta ANC a garin Ekurhuleni kusa da birnin Johannesburg, Ramaphosa ya ce gwamnatinsa ta “damu sosai” kan cewa “kusan kowace rana” Isra’ila tana keta yarjejeinyar ranar 10 ga watan Oktoba da ta ƙulla da Hamas duk da cewa yarjejeniyar ta taimaka wajen sako waɗanda Hamas ta kama da kuma fursunonin siyasar Falasɗinawa daga hannun Isra’ila.

Ya ce matakin ɓarnar da aka yi a Gaza, wanda Afirka ta Kudu ta yi imanin cewa kisan ƙare dangi ne, ya tilasta wa Pretoria ta shigar da ƙara kan Isra’ila a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICJ) a watan Sabumban shekarar 2023.

Tun wancan lokacin, kotun hukunta manyan laifukan ta fitar da matakai na wucin gadi da ke umartar Isra’ila ta hana daukar matakan da za su iya kasancewa kisan ƙare dangi.

“Tun lokacin da aka fara farmakin ranar 7 ga watan Oktoba na shekarar 2023, fiye da mutum 70,000 ne aka kashe a Gaza, inda yawancinsu mata ne da ƙananan yara,” in ji Ramaphosa.

Ya jaddada buƙatar Afirka ta Kudu ta tsagaita wuta nan take da kuma samar da wani shirin siyasa da zai samar wa Falasɗinawa ƙasa mai cin gashin kanta a gefen Isra’ila. 

Yaƙe-yaƙe a Sudan da Yukrain

Ya kuma faɗaɗa kiraye-kirayensa kan sauran rikice-rikice na duniya inda ya yi Allah wadai da “mummunar wahalar ” da yaƙin basasar Sudan ya janyo, inda rahotanni suka ce fiye da mutum 150,000 sun mutu, da kuma ƙara jaddada hannun Afirka ta Kudu a ƙoƙarin samar da zaman lafiya da ke da alaƙa da yaƙin Rasha da Yukrain.

Ramaphosa ya bayyana balaguron samar da zaman lafiya na shugabannin Afirka da shi ya jagoranta shekaru biyu da suka gabata zuwa biranen Kiev da St. Petersburg, domin neman Rasha da Yukrain su bi hanyar tattaunawa.

Rikicin ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.