AfDB zai ba Nijar CFA biliyan 98.7 domin magance matsalar ruwa ta shekara 70 a Zinder

Firaministan Nijar Ali Mahaman Zeine ya bayyana girman matsalar ruwa a wannan yankin wadda ya ce matsala ce tun ta zamanin mulkin mallaka, ya kuma ce ko tashar samar da ruwa ta farko ta Aroungouza wadda aka gina a 1955 ba ta taɓa magance matsalar ba.

By
AfDB ya amince domin bayar da kimanin CFA biliyan 98.7 domin sake gina hanyoyin samun ruwan sha da tsaftar muhalli.

Bayan shafe shekaru 70 ana fama da ƙarancin ruwa da kuma samar da mafita maras ɗorewa lokaci bayan lokaci, da alamu yankin Zinder da kewaye ya samu mafita ta dindindin

Bankin Ci gaban Tattalin Arzikin Afirka AfDB ya amince domin bayar da kimanin CFA biliyan 98.7 domin sake gina hanyoyin samun ruwan sha da tsaftar muhalli.

Waɗannan maƙudan kuɗaɗen ba Zinder kaɗai za ta amfana da su ba, har da Mirriah da wasu ƙauyuka 14 da ke maƙwabtaka, wanda yawan jama’arsu ya kai mutum 700,000 inda fiye da rabinsu mata ne.

Ga waɗannan al’ummomin da suka daɗe suna wahala, ruwa — wanda ya kasance yana musu matuƙar wahalar samu kuma mai matuƙar muhimmanci — a ƙarshe zai iya zama abin da za su iya samu cikin sauƙi sannan kuma ya kasance wani jigo na samun ci gaba, tare da kawo ƙarshen matsalar ruwan da ta yi tasiri matuƙa a ɓangaren lafiya da tattalin arziki da rayuwar yau da kullum ta jama’a tsawon shekaru.

A jawabin da ya gabatar, Firaiministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine bai yi ƙoƙarin rage girman matsalar ba. Ya bayyana ta a matsayin wata “matsala da ta addabi yankin tun zamanin mulkin mallaka,” wadda ma tashar farko ta shan ruwa ta Aroungouza, wadda aka gina a 1955, ba ta taɓa magance ta gaba ɗaya ba.

Zinder, birni na biyu mafi girma a ƙasar, ya shafe shekaru yana fama da wannan matsala, yayin da jama’a ke ƙaruwa, albarkatu suna raguwa, kuma illolin sauyin yanayi na ƙara bayyana.

“Babban burin wannan aikin shi ne inganta rayuwar jama’ar Zinder cikin ɗorewa,” in ji shi. “Zai magance buƙata ta haƙiƙa, buƙata mai muhimmanci ga mutanen wannan birni da na yankunan da ke kewaye, waɗanda tsawon shekaru suke fama da ƙarancin ruwa,” in ji Zeine.