Shugaban Amurka Donald Trump ya ce rundunar Amurka ta ceto direban jirgin sama na biyu wanda Iran ta harbo inda ya bayyana ceton a matsayin "daya daga cikin mafi jarumtar ayyukan ceto a tarihin Amurka".
"Wannan jarumin ya kasance a gefen abokan gaba a cikin duwatsu masu haɗari na Iran, ana farautarsa da maƙiya," in ji Trump a shafinsa na Truth Social a ranar Lahadi.
"Ya ji raunuka, amma zai samu lafiya."
"Wannan aikin ceton mai ban mamaki ya zo ne a ƙarin nasarar ceto wani jarumin matukin jirgi, jiya, wanda ba mu tabbatar da shi ba, domin ba ma son jefa aikin ceto n biyo cikin hadari hadari."
Sojan saman shi ne mutum na biyu daga cikin ma'aikatan biyu na jirgin F-15 wanda Iran ta ce, a ranar Juma'a, ta harbo shi.
Sanarwar ta fito ne yayin da Iran ta harba makamai masu linzami da na'urorin jiragen sama marasa matuƙa kan Isra'ila da Kuwait a safiyar Lahadi, kuma rana ɗaya bayan Trump ya ce Iran na da awanni 48 don cim ma yarjejeniya ko ta fuskanci "babban bala’i".
Sojojin Amurka sun bar Iran bayan aikin ceto
Rundunar Sojin Amurka ta ƙaddamar da ayyuka da dama a cikin Iran a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gano direbobin jirgin waɗanda suka fice daga jirgin bayan Iran ta harbo shi inda sojojin suka tuntuɓi hedkatarsu ta hanyar hanyoyin sadarwarsu.
Jami'ai sun ce an ceto matukin jirgi cikin 'yan awanni bayan an harbo jirgin, yayin da ya ɗauki fiye da rana guda kafin a gano matuƙin na biyu. Ɗaya daga cikin jami’an Amurka ya ce aikin ya haɗa da dakaru na musamman inda suka samu taimakon jiragen sama.
A yayin yunƙurin ceton a ranar Juma'a, dakarun juyin juya hali na Iran sun habo jirgin helikwafta na Amurka duk da cewa jirgin ya tsira.












