| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Dalibai tara sun gurfana a gaban kotu kan tayar da gobara a wata makaranta a Kenya
Masu bincike sun nemi a ƙara musu lokaci don bincika ken musabbabin mummunar gobarar da ake zargin kafita ce da aka cinna wa wuta ta haifar.
Dalibai tara sun gurfana a gaban kotu kan tayar da gobara a wata makaranta a Kenya
Ana sa ran samun sakamakon gwajin DNA da aka yi don gano asalin gawarwakin da suka ƙone a ranar Laraba. / AP

Dalibai tara da ake zargi da tayar da gobara wadda ta yi sanadiyar mutuwar 'yan mata 16 a wata makaranta da ke tsakiyar Kenya sun gurfana a gaban kotu ranar Talata.

Masu bincike sun nemi a ƙara musu lokaci don bincika ken musabbabin mummunar gobarar.

Kotun Koli da ke garin Naivasha, mai nisan kilomita 90 (mil 55) yamma da babban birnin Nairobi, ta ce za ta yanke hukunci a ranar Laraba kan ko za a iya tsare 'yan matan na tsawon wata guda yayin da ake kan bincike.

Gobarar da ta faru a ranar 28 ga Mayu ta ratsa ɗakin kwanan dalibai na Kwalejin 'Yan Mata ta Utumishi wanda ke ɗauke da ɗalibai 202. Matron ɗin makarantar ta kasa buɗe ƙofar da wuri, lamarin da ya tilasta wa ɗaliban su nemi mafita wajen tsarewa ta ƙofa ɗaya, a cewar masu bincike.

Cinna wa katifa wuta

'Yanmatan da ake zargin da aikata wannan mummunan aiki sun shafe kwana biyar a hannun 'yan sanda, a lokacin da aka yi musu tambayoyi, an gano cewa gobarar ta tashi ne sakamokon cinna wuta kan katifar da ke bakin ƙofar ɗakin kwanan daliban ta amfani da ashana da karanzir. Ko da yake ba a bayyana wani dalili da haifar da hakan ba zuwa yanzu.

Ana sa ran samun sakamakon gwajin DNA don gano asalin wasu gawarwakin da suka ƙone da ba za iya tantance su a ranar Laraba.

Hotunan na’urar CCTV da aka samu daga ɗakin kwanan daliban sun nuna ɗalibai shida suna kunna wutar jim kaɗan kafin sauran ɗaliban su farka, kana sun gaggauta tserewa daga gobarar wadda ta yi sanadiyyar jikkata mutane 79.

Tun bayan faruwar lamarin, an sake samun wasu ƙarin gobara a makarantu guda biyar a sassa daban-daban na ƙasar, kuma tun daga farkon shekarar nan hukumar Red Cross ta Kenya ta kai daukin gaggawa ga makarantu 37 da suka samu iftila’in gobara. Ba a samu asarar rai daga ko daga ko ɗaya daga cikin gobarar da aka samu.

Yawan gobara a makarantu

Ana yawan samun gobara a makarantu a Kenya, inda azuzuwa da ɗakunan kwanan dalibai galibi suke cike da jama'a kuma ba kasafai ake samun kayan aiki na kashe gobara ba.

Mafi munin lamarin da aka samu ya faru ne a shekarar 2001, lokacin da ɗalibai 67 suka mutu a gundumar Machakos, sai kuma wanda ya faru a shekarar 2024, lokacin da yara 21 suka mutu a gundumar Nyeri.


Kazalika an yi ta samun rahotannin cewa dalibai suna kona makarantu soboda ladabtar da su da ake yi.

 

Rumbun Labarai
Ghana ta kwashe 'yan ƙasarta 300 daga Afirka ta kudu yayin da ake zanga-zanga kan baƙin haure
Mutane uku sun mutu bayan motar fasinja ta yi karo da giwa a gandun dajin Uganda
Shugaban Senegal Faye ya naɗa sabon firaminista da zai maye gurbin Sonko
Adadin mutanen da Ebola ta kashe a Jamuhuriyar Kongo ya wuce 200
Shugaban Senegal Faye ya sallami Firaministansa Ousmane Sonko
Kenya za ta rage farashin man dizel bayan zanga-zangar da aka yi kan tsadar makamashi
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar za ta ƙayyade kuɗin gidajen haya
Sierra Leone ta amince ta karɓi kashin farko na waɗanda aka taso ƙeyarsu daga Amurka
'Makashin Al Fasher' ya koma fagen daga a yaƙin Sudan: Rahoto
Nijar da China sun cim ma yarjejeniyar mai bayan watanni ana takaddama
Adadin mutanen da suka mutu a Congo saboda kamuwa da Ebola ya kai 131
Kenya ta kama wata mata bisa zargin damfarar Ba’amurke dala 431,000 a yarjejeniyar cinikin zinare
Dole Afirka ta daina bin umarnin manyan ƙasashen duniya
WHO ta bayyana ɓarkewar Ebola a Jamhuriyar Kongo a matsayin 'matsalar lafiya ta gaggawa'
Mutum 80 sun rasu a sabuwar ɓarkewar Ebola a Jamhuriyar Congo
Sojojin Sudan sun ƙwace iko da wani muhimmin birni a kusa da iyakar Habasha bayan arangama da RSF
Yakin Sudan: Yara na daga gomman da aka kashe a arangamar makonni biyu a Kordofan
Nijar na son ƙara adadin jihohinta daga 8 zuwa 19 da kuma sauya sunayen wasu jihohim
Shirin 'Big Catch-Up': Kokarin da ya kawo alluran rigakafi miliyan 100 ga yaran Afirka da aka manta
Ghana za ta kwashe ɗaruruwan 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu bayan hare-haren ƙin jinin baƙi