Fidan na Turkiyya zai halarci bikin sa hannu na 'Hukumar Zaman Lafiya' ta Gaza a Switzerland

Babban jami'in diflomasiyyar Turkiyya Hakan Fidan zai halarci bikin a ranar Alhamis a Suwizalan, a madadin Shugaba Recep Tayyip Erdogan, in ji ma'aikatar harkokin wajen.

By
Hakan Fidan zai halarci taron a ranar Alhamis a madadin Shugaba Recep Tayyip Erdogan. / AA Archive

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, zai halarci bikin sanya hannu kan kundin Majalisar Zaman Lafiya na Gaza a Switzerland.

Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta faɗa a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba cewa Hakan Fidan zai halarci bikin a ranar Alhamis a madadin Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Kafa majalisar na zuwa ne daidai da kaddamar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta, wanda aka tsara don dakatar da yaƙin Isra'ila a Gaza, wanda ya kashe mutane sama da 71,000 kuma ya jikkata sama da 171,000 tun Oktoba 2023.

'Kwamitin Zaman Lafiya'

A ranar Juma'a da daddare, Fadar White House ta sanar da kafa Kwamitin Zaman Lafiya tare da amincewa da Kwamitin Kasa na Gudanarwar Gaza, ɗaya daga cikin hukumomi huɗu da aka tsarara don jagorantar sauyi a yankin cikin matakai.

Kwamitin, wanda ake sa ran Shugaba Trump zai jagoranta, zai haɗa da kusan shugabannin ƙasashe 15; zai sa ido kan gwamnatin ƙwararru ta Falasdinawa wadda har yanzu ba a kai ga kafawa ba, zai kula da aikin sake gina Gaza.

Kasashen da ake sa ran za su shiga kwamitin sun haɗa da Turkiyya, da Birtaniya, da Jamus, da Faransa, da Italiya, da Saudiyya, da Qatar da Masar, kuma tsohon jakadan MDD na yankin Gabas ta Tsakiya, Nikolay Mladenov, na iya zama wakilin Kwamitin Zaman Lafiya a wurin.

Wannan yunƙuri wani ɓangare ne na shirin Trump da ya gabatar mai saɗara 20, wanda Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi bisa Kuduri na 2803 a watan Nuwamban 2025.