Kuna tunanin Gasar Kofin Duniya ta 2026 batu ne na sanannun ‘yanwasa irinsu Lionel Messi, Kylian Mbappé, da Erling Haaland kawai? Idan kun lura da kyau, akwai wasu 'yan wasa a gasa da ke bin sawun iyayensu, waɗanda tsaffin 'yanƙwallon ne a duniya.
Wasu cikin ‘yanwasan na yanzu suna amsa mashahuran sunayen iyayensu, yayin da wasu suka yanke hukuncin amsa sunan da za su gina shuhara ta ƙashin-kansu.
Luca Zidane – Aljeriya
Mai tsaron gidan Aljeriya, Luca Zidane, ɗa ne gun tsohon kyaftin ɗin tawagar Faransa, Zinedine Zidane, wanda mashahurin ɗanwasa ne da ya jagoranci tawagar ta Les Bleus, a Gasar Kofin Duniya ta 1998.
Shekaru ashirin da suka wuce, Zidane uba ya bar fagen gasar bayan samun jankati a wasan ƙarshe na 2006 tare da Italiya. Yanzu, ɗansa ya dawo da sunan Zidane a babbar gasar, amma wannan karon yana buga wa Aljeriya, ƙasar kakanninsa.
Zidane ƙarami ma ya yi karo da Lionel Messi na Argentina, wanda wani ƙalubale ne da mahaifinsa ya san da shi sosai a zamanin wasansa.
Marcus Thuram – Faransa
Marcus Thuram ɗa ne na Lilian Thuram, ɗaya daga cikin manyan masu tsaron baya na Faransa, kuma abokin wasan Zinedine Zidane a tawagar da ta lashe Kofin Duniya na 1998.
Yayinda mahaifinsa ya yi suna a ɓangaren tsaron baya, Marcus ɗanwasan gaba ne. Yana wasan a Inter Milan kuma ya zama wani muhimmin ɓangare na masu kai hari a tawagar Faransa, inda yake gini kan tarihin da Thuram ya gina a Faransa.
Mostafa Shobeir – Masar
A gaban raga Masar akwai gola Mostafa Shobeir, ɗan tsohon gollan tawagar ƙasar, Pharaohs, wato Ahmed Shobeir, wanda ya wakilci Masar a Kofin Duniya na 1990 a Italiya.
Fiye da shekaru talatin da suka wuce, ga wani Shobeir ɗin buga Kofin Duniya. Matashin golan ya nuna kansa a fagen duniya cike da jarumtaka a wasansu da Belgium, inda ya hana abokan karawa cin ƙwallo, kuma ya taimaka wa Masar samun sakamako mai muhimmanci.
Timothy Weah – Amurka
Timothy Weah ba ya wakiltar ƙasar mahaifinsa, Liberia, amma yana ɗauke da ɗaya daga cikin shahararrun sunayen ‘yanƙwallon Afirka.
Babansa George Weah, shi kaɗai ɗan Afirka da ya taɓa lashe kyautar Ballon d’Or kuma tsohon shugaban Liberia ne. Timothy ya zama muhimmin ɗanwasan tawagar Amurka.
Duk da cewa mahaifinsa bai samu damar buga gasar Kofin Duniya ba, ɗansa yana tabbatar da wannan mafarki kuma yana ci gaba da gadon Weah a babban mataki na duniya.
Justin Kluivert – Netherlands
Justin Kluivert na bin sawun mahaifinsa, Patrick Kluivert, ɗaya daga cikin manyan maciya ƙwallo na Netherlands, kuma tauraro a tawagar Dutch da ta kai zangon samifainal na Kofin Duniya a 1998.
A yanzu Justin yana wakiltar tawagar Oranje a gasar bana, ina yake rubuta nasa babin a ɗaya daga cikin shahararrun labaran dangi ‘yanƙwallo a Netherlands.
Giuliano Simeone – Argentina
Giuliano Simeone na Argentina, ɗan Diego Simeone ne, wanda ɗanwasan tsakiya ne da ya wakilci Argentina a gasar Duniya har sau uku kafin ya zama ɗaya daga cikin ƙwararrun koci-koci a duniya.
Simeone ƙarami ya gaji azama da ƙwazo na mahaifinsa, kuma a yanzu yana ƙirƙirar nasa tarihin sanye da jesin mai bulu da fari ta Argentina.
Nico Paz – Argentina
Wani ɗan Argentina mai ɗauke da mashahurin shi ne Nico Paz. Mahaifinsa, Pablo Paz, ya kasance a tawagar Argentina ta Kofin Duniya na 1998 a Faransa. Kusan shekaru talatin bayan nan, Nico ya bi gadon gidansu kuma ya zo gasar Kofin Duniya.
Francisco Conceição – Portugal
Francisco Conceição na Portugal ɗan tsohon ɗanwasan gefe, Sérgio Conceição ne, wanda ya wakilci Portugal a Kofin Duniya na 2002.
Francisco na da sauri, fasaha, da rashin tsoro, kuma yanzu yana cikin sabon ƙarni na tawagar Portugal yayin da yake ƙoƙarin kafa kansa a matakin duniya.
Kristian Thorstvedt – Norway
Kristian Thorstvedt, ɗanwasan tsakiya ne na Norway, kuma yana bin sawun mahaifinsa Erik Thorstvedt, wanda ya kasance golan Norway a Kofin Duniya na 1994 a Amurka. Fiye da shekaru 30 bayan nan, wani Thorstvedt ɗin yana buga wannan gasa ta duniya.
Giovanni Reyna – Amurka
Giovanni Reyna ya fito daga ɗaya cikin dangin ‘yanƙwallo a Amurka mafiya ƙwarewa. Mahaifinsa, Claudio Reyna, ya jagoranci Amurka kuma ya buga a gasar Kofin Duniya sau uku.
A yanzu Giovanni yana riƙe da sunan dangin a wannan sabon zamani. Ya zama ɗaya daga cikin manyan fuskokin ƙwallon ƙafa a Amurka.
Erling Haaland – Norway
Ɗaya daga cikin manyan taurarin Kofin Duniya na 2026, Erling Haaland na bin sawun mahaifinsa, Alf-Inge Haaland, tsohon ɗanwasan Norway wanda ya wakilci ƙasarsa a 1994. Kamar mahaifinsa, Erling ma ya yi fice a Manchester City.
Yayin da Alf-Inge ya yi shekaru uku tare da City, tsakanin 2000 da 2003, ɗansa ya zama ɗaya daga cikin manyan masu zura ƙwallo na kulob ɗin a yau, inda ya taimaka wa City lashe kofuna a cikin gida da kuma Turai.
Erling yana jagorantar ‘yanwasan gaba na Norway a Kofin Duniya a bana, kuma ba wai kawai yana ɗaukar sunan Haaland ba ne a sabon zamani, har ma yana gina tarihin da zai iya wuce nasarorin mahaifinsa a wasan ƙwallon ƙafa.
Daga Zidane zuwa Shobeir, daga Thuram zuwa Kluivert, 'ya'yan mashahuran tsaffin ‘yanƙwallon suna nunawa duniya cewa baiwa na iya gudana a zuriya. Wato kowane ƙarni na kafa tarihinsa a Kofin Duniya.













