Wani hari mai muni da ‘yanbindiga suka kai ya tarwatsa wani ɗaurin aure a ƙauyen Kahir da ke ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna a arewacin Nijeriya, inda ya kashe aƙalla mutane 13 tare da garkuwa da wasu da dama.
Rundunar ‘yansandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin da ya jikkata wasu mutane, tana mai cewa tana kan tattara bayanai game harin ciki har da adadain waɗanda aka sace.
Wani shugaban alu’umma, Musa Adamu, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:47 na dare ranar Lahadi.
Ya ce maharan, waɗanda suka je da yawa ɗauke da muggan makamai, sun afka wa wurin inda suka fara harbin kan-mai-uwa-da-wabi ga baƙin cikin ɗakin taron.
Wasu daga cikin waɗanda suka halarci bikin sun ji rauni daga harbin bingida kuma an garzaya da su asibitin gwamnati da ke Kagarko, yayin da aka tura waɗanda rauninsu ya yi yawa asibitoci a birnin Kaduna.
Mazauna yankin sun ce ‘yabindigan sun shafe kusan sa’a ɗaya suna aika-aikar ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Rahotanni sun ce sun saci kayayyakin abinci da kayayyakin masaraufi a shagunan da ke kusa tare da ɗauke magunguna daga wani kantin magani.
Tuni dai aka fara neman maharan domin kama su da kuma hukunta su, in ji hukumomin ‘yansanda.
Jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin Arewa Maso Yammacin ƙasar da ke fama da hare-haren ‘yanbindiga.
Sauran jhohin sun haɗa da Sokoto da Kaduna da Kebbi da Zamfara da kuma Katsina.
A jihohin Sokoto da Kebbi, ana ɗora alhakin kai hare-hare kan ƙungiyar ‘yanta’adda ta Lakurawa.
Mambobin ƙungiyar suna kai samame daga maɓoyarsu a cikin dazuka inda suke sace dabbobi da kuma ƙaƙaba “haraji” kan mutane.
Gwamnatin tarayya, tare da sojin Amurka sun ƙaddamar da harin sama a jihar Sokoto a lokacin bikin Kirsitimetin da ya gabata a kan mambobin ƙungiyar.
Kazalika Nijeriya na fama da da sauran ƙungiyoyin ‘yanbindiga da suka ruɓanya ƙalubalen tsaronta a arewacin ƙasar.
Matakan soji ba su samar da sakamako na a zo a gani ba.
Rikicin ya bazu zuwa ƙasashen Nijar da Chadi da Kamaru masu maƙwabtaka, lamarin da ya sa aka kafa wata rundunar soji ta haɗin gwiwa domin yaƙar ƙungiyoyin.
Amma haɗakar ta yi sanyi cikin ‘yan shekarun nan bayan Nijar ta fice sakamakon rikicin diflomasiyya da Nijeriya bayan juyin mulkin shekarar 2023 a ƙasar Nijar.
Da farkon wannan watan, Amurka ta fara tura dakaru Nijeriya domin ba da tallafi na fasaha da horaswa ga sojin ƙasar wajen yaƙar ƙungiyoyin ‘yanta’adda.
Rundunar sojin Amurka a Afirka ta ce ana tsammanin dakaru 200 su kasance cikin waɗanda za a tura domin aikin.











