Shugaba Mahama ya yaba wa Amurka kan cire harajin da ta sa kan kayayyakin gona na Ghana

Shugaban Ghana ya ce kayayyakin gona na Ghana waɗanda ake kaiwa Amurka da suka haɗa da koko, avokado, lemu, barkono, albasa da doya, a yanzu ba za a rinƙa saka musu haraji ba.

By
Shugaba Mahama ya yi wannan jinjina ne a jawabinsa a bikin Ranar Manoma ta 41 da aka gudanar a Ho da ke Jihar Volta. / John Mahama Facebook

Shugaba John Dramani Mahama ya yaba wa Gwamnatin Amurka saboda cire harajin da ta kakaba kan kayayyakin amfanin gona da ake shigowa da su daga Ghana.

Ya ce harajin da aka kakaba ya shafi kayayyakin noma kamar koko, avokado, lemu, barkono, albasa da doya, yana bayyana cewa janye wannan mataki na nufin kayayyakin Ghana da ake kaiwa kasuwar Amurka yanzu ba za su sake fuskantar wani haraji ba.

Shugaba Mahama ya yi wannan jinjina ne a jawabinsa a bikin Ranar Manoma ta 41 da aka gudanar a Ho da ke Jihar Volta.

“Ba mu biyan wani haraji. Yawan cinikayyar mu da Amurka a kayayyakin noma yanzu ya kai kusan dala miliyan 100, amma za mu iya ƙara wannan sosai saboda damar da suke ba mu,” in ji shi.

Ya shawarci masu aikin noma da su duba jerin kayayyakin noman Ghana da ake fitarwa zuwa Amurka, domin su ƙara inganta ƙarfin samar da su don fitarwa da kuma samun ƙarin kuɗaɗe.

Shugaba Mahama ya bayyana cewa noma yana da riba kuma yana ƙara samun kuɗi, shi ya sa har a matsayinsa na Shugaba, yana ci gaba da kasancewa a matsayin manomi.

Ya ƙarfafa dukkan masu mukami da jami’an gwamnati da su sayi fili su shuka miskin mai (oil palm).

Haka kuma shugaban ya ƙarfafa gwiwar masu riƙe da muƙaman gwamnati da su samu gona su shuka kwakwar manja.

“Idan ka yi kadada 10 ko 20 na kwakwar manja, za ka yi mamakin yadda zai ba ka kuɗi fiye da albashin da kake karɓa a duk shekara,” in ji shi.

Shugaban ya roki ’yan Ghana da su zuba jari a cikin noma kuma su yi ƙoƙarin samar da isasshen amfanin gona domin su ƙara samun kuɗin shiga.”