| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Iran ta yi gargaɗin cewa yaƙi da Amurka nan gaba zai iya shafar duka shiyyar da ma fannin makamashi
Kakakin rundunar sojin Iran, Mohammad Akraminia, ya bayyana cewa cibiyoyin makamashi da na sadarwa na iya zama wuraren da za a kai wa hari a kowanne irin rikici da za a iya yi a nan gaba.
Iran ta yi gargaɗin cewa yaƙi da Amurka nan gaba zai iya shafar duka shiyyar da ma fannin makamashi
Wajen da Iraniyawa suka yi da'awar an harbo jirgin Amurka na sufuri da masu saukar ungulu biyu da suka je ceto a Isfahan, Iran, a Afrilun 2026. / AP

Wani kakakin rundunar sojin Iran ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Amurka a nan gaba zai iya bazuwa a faɗin yankin, har ma ya shafi cibiyoyin makamashi da na sadarwa.

Birgediya Janar Mohammad Akraminia, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Mehr a ranar Laraba cewa Iran ta riga ta yi gargaɗi a baya cewa idan abokan gabanta suka yi kuskuren kai mata hari, to za ta mai da martani nan-take kuma hakan zai jefa gaba ɗaya yankin cikin tashin hankali.

“Yaƙi a nan gaba zai iya shafar sabbin yankuna,” in ji Akraminia.

Yana ishara zuwa mashigar tekun ta Bab al Mandeb da kuma sansanin Amurka da ke Siriya, yana cewa dukansu sun zama bangaren rikicin duk da cewa a baya ba sa cikin taswirar rikicin.

“A yau, akwai barazana a faɗin shiyyar baki ɗaya, kuma muna da damar da zamu iya fuskanta da kuma tunkararsu,” in ji shi.

Cibiyoyin Makamashi da Sadarwa

Akraminia ya ce yaƙi a nan gaba zai iya buɗe sabbin fagen daga, ciki har da cibiyoyin makamashi da na sadarwa a faɗin shiyyar.

Ya fito fili ya ambaci cibiyoyin makamashi da layukan sadarwa da yawancinsu ake gudanarwa a ƙarƙashin teku a ruwan da ke tsakanin Iran da ƙasashen Larabawa, har ma da ta Tekun Oman.

“Duk inda abokin gaba yake da bukatunsa, muddin aka takale mu, za su iya faɗawa ƙarƙashin halastattun wuraren da dakarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran za su iya kai wa hari,” in ji shi.

Akraminia ya kuma buƙaci Qatar da ta ƙara ƙoƙari wajen tantance matsayin matuka jiragen saman Iran guda uku da suka ɓace tun bayan wani harin da sojojin saman Iran suka kai a sansanin Amurka da ke Qatar ranar 2 ga Maris.

Ya ce jiragen saman Iran biyu nau’in Sukhoi ne suka kai harin a sansanin kafin a harbo su lokacin da suke kan hanyar dawowa. Daga baya an gano gawar daya daga cikin matuƙan jirgin su huɗu, Majid Kazemi, yayin da har yanzu ba a ga sauran uku ba.

Qatar ta musanta riƙe matuƙan jirgin su uku, tana mai cewa dakarunta na neman agaji sun gano gawar matuƙin jirgi ɗaya, amma ba su sami shaidar cewa an kama sauran ba.

Waɗannan kalamai na zuwa ne a yayin da ake tsakiyar takun-saƙa tsakanin Iran da Amurka, wanda ya faro tun ranar 28 ga Fabrairu da hare-haren Amurka da Isra’ila a kan Iran, sannan daga baya suka faɗaɗa a shiyyar yayin da Iran ta maida martani kan sansanonin sojin Amurka.

Daga baya faɗan ya bazu zuwa fagagen daga daban-daban na shiyyar sannan ya kawo cikas ga tafiye-tafiyen teku kafin daga bisani Iran da Amurka suka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a ranar 17 ga Yuni ta hanyar shiga tsakanin Qatar da Pakistan don kawo karshen yaƙin da kuma shimfiɗa hanyar tattaunawa.

Tun daga wancan lokacin Iran take zargin Amurka da rashin cika yarjejeniyar sosai, yayin da Qatar da Pakistan ke ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya tsakanin ɓangarorin biyu.