Jerin lokutan da aka shafe ana shari'ar Nnamdi Kanu, jagoran 'yan a-waren Biafra a Nijeriya
An fara kama shi ne a shekarar 2015 bisa zarginsa da laifin cin amanar kasa da kuma zama mamba na kungiyar da ba ta kan ka’ida.
Bayan shekaru goma ana shari’o’i a kotuna daban-daban da sauya alkalai, da bayar da beli da saɓa sharuɗɗan belin, da guduwa da sake kamo shi, a karshe babbar kotun Nijeriya ta yanke wa jagoran ‘yan a-waren Biafra Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai saboda samun sa da laifin ta’addanci.
Hankula sun fara karkata kan Kanu ne a shekarar 2009 lokacin da ya fara watsa shirye-shirye ta gidan rediyon ‘Radio Biafra’ da ke birnin Landan.
An fara kama shi ne a shekarar 2015 bisa zarginsa da laifin cin amanar kasa da kuma zama mamba na kungiyar da ba ta kan ka’ida.
Shari’ar Nnamdi Kano cike take da rudani har zuwa lokacin daurin aka yanke masa hukunci, kuma a iya cewa har yanzu da sauran rina a kaba, tun da bangarensa sun ce za su daukaka kara.
Ga wasu muhimman abubuwa da suka shafi kamu da kuma shari’ar Nnamdi Kanu.
An fara kama shi ne a watan Oktoban 2024 a birnin Legas, wato shekaru 11 da suka gabata.
An fara gurfanar da shi a ranar 23 ga watan Nuwamban 2015 a wata kotu a Abuja bisa tuhumar hada baki wajen aikata manyan laifuka da cin zarafi da kasancewa ɗan haramtacciyar kungiyar IPOB.
A Disamban 2025 aka ƙara tuhume-tuhumen zuwa shida da suka hada da cin amanar kasa, shigo da na’urar watsa shirye-shirye ta rediyo ba bisa ƙa’ida ba, da kuma ɓata wa Marigayi Shugaba Buhari suna.
An bayar da belinsa a Afrilun 2017 saboda dalilan rashin lafiya.
A Satumban 2017 sojoji sun kai farmaki gidansa a Jihar Abia a yunkurin dakile ayyukan kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra da ɓallewa daga Nijeriya, inda daga nan ya yi batan dabo ya kuma saba ka’idojin beli.
A Maris din 2019, Mai Shari’a Binta Nyako ta soke belin da ta ba shi sannan ta bayar da umarnin kama shi.
A watan gwamnatin tarayya ta samu umarnin kotu na ba da damar ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci tare da haramta ta.
A Fabrairun 2018 ta yi umarnin a ware shari’ar Nnamdi Kanu daga sauran wadanda aka tuhume su tare.
A Nuwamban 2020, wata Kotun Tarayya ta fara shari’ar Nnamdi Kanu a bayan idonsa.
A Janairun 2021, an ci gaba da shari’ar Kanu, sai dai shi da lauyansa ba wanda ya halarta.
A ranar 19 ga watan Yunin 2021, an sake kama Nnamdi Kanu a Kenya, aka mayar da shi Nijeriya.
A watan Yunin 2021 kotu ta tsare Kanu a hannun DSS a Abuja.
A Afrilun 2022, Babbar Kotun Tarayya ta soke tuhume-tuhume 8 daga cikin 15 da ake yi wa Kanu.
A watan Oktoba kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke duka tuhume-tuhumen da ake yi masa, tare da ba da umarnin sakinsa nan-take.
A Disamba kuma kotun Koli ta soke hukuncin kotun daukaka karar, sannan ta dawo da tuhume-tuhume bakwai da ake yi masa kan ta’addanci.
A Maris 2025 Alkali James Omotosho ya karbi ci gaba da shar’iar, kuma kotun ta umarci gaggauta shari’ar.
A Oktoban 2025 Kanu ya kori lauyansa, ya ce shi ne lauyan kansa.
A ranar 24 ga Oktoban 2025 kotun ta dage shari’ar ta Kanu bayan ya ce ba zai iya ci gaba da kare kansa ba saboda lauyoyinsa ba su ba shi fayel din shari’ar ba.
Kwana uku bayan hakan Kanu ya shaida wa kotun cewa ya duba fayel dinsa, kuma bai ga wata tuhuma da ake masa ba, sannan ya ƙi kare kansa, ko kiran shaidu.
A ‘yan kwanakin da suka biyo baya, an yi ta sa-toka-sa-katsi tsakanin Nnamdi Kanu da kotun da suka hada da mika bukatar soke duka tuhume-tuhumen da ake yi masa, saboda babu dokar da za ta iya yi masa shari’a, da ba shi damar karshe da Mai Shari’a Omotosho ya yi don ya kare kansa.
Da ba shi dama da ƙara ɗaga masa ƙafa kan ya kare kansa, har zuwa lokacin da kotun ta ce, ya rasa duk wata dama ta kare kansa, sannan kotun ta sanya ranar 20 ga Nuwamba don yake hukunci.
A ranar Alhamis din ne kuma, kotun ta same shi da laifin ta’addanci da kasancewa mamban Harmatacciyar Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra (IPOB), bayan wata ‘yar hatsaniya.
Sannan aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifi a duka tuhume-tuhume bakwai da aka yi masa. Kuma a cewar alkalin a hakan ma an yi sassauci ne, domin laifukansa na hukuncin kisa ne.
To amma fa shari’a ba ta ƙare ba, domin tuni masu bai wa Nnamdi Kanu din shawara suka ce za su dauka kara kara zuwa Kotun Daukaka Kara, kuma za su tafi har zuwa Koton Koli.