Yayin da farashin mai ke ƙaruwa a yanayin tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, ƙasashe da dama na Asiya sun koma aiki daga gida kuma daga nesa don rage matsi na buƙatar makamashi da kuma kare tattalin arziki mai rauni.
Ƙasashe ciki har da Indonesia, Vietnam, Thailand da Philippines sun fara aiwatar da tsarin aiki daga gida da matakan kiyayewa kamar irin na lokacin ɓullar cutar COVID-19.
A Indonesia, hukumomi suna la’akari da tsarin aiki na fasaha har ma da karatu ta yanar intanet don rage yawan amfani da mai. Rage zirga-zirga zai taimaka wajen rage yawan amfani da mai da kashi 20%, a cewar kafar Jakarta Globe.
Vietnam, wacce ta dogara sosai kan man fetur da ake shigo wa da shi daga ƙasashen waje, ta yi kira ga 'yan kasuwa da su rungumi aiki daga nesa bayan hauhawar farashin mai da dizal ya haifar da dogayen layuka a tashoshin mai.
"Ana buƙatar a ƙarfafa wa Kasuwanci gwiwa ta hanyar aiki daga gida idan zai yiwu don rage tafiye-tafiye da zirga-zirga ababen hawa," kamar yadda Ma'aikatar Kasuwanci ta kasar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a tsakiyar watan Maris.
Tuni Thailand ta mayar da sassan ɓangaren ma’aikatun gwamnatin ƙasar zuwa aiki daga nesa, tare da matakan adana makamashi kamar iyakance yin amfani da na'urar sanyaya iska da rage tafiye-tafiye na gwamnati.
A ƙasar Philippines, an sassauta tsarin zuwa aiki, sannan wasu ma'aikatan gwamnati za su ringa zuwa ofis a kwanaki huɗu.
A ranar Talata, Shugaba Ferdinand Marcos Jr. ya ayyana dokar ta-baci kan makamashi a ƙasar, inda ya sanya matakan daidaita kayayyaki da kuma kare tattalin arziki daga hauhawar farashin mai.
A ɓangare guda kuma, Pakistan ta aiwatar da wasu daga cikin mafi tsaurin matakai a yankin, ciki har da aiki daga nesa na wani lokaci ga ma'aikatan gwamnati, da rage alawus ɗin da ake bayarwa na mai da kuma rufe makarantu na wucin-gadi.
Mashigar Hormuz
Matakan na zuwa ne yayin da kasuwannin makamashi na duniya ke fuskantar barazana sakamakon rikicin da ke ci gaba da faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Tun daga ranar 28 ga Fabrairu Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare ta sama kan Iran, inda suka kashe mutane sama da 1,340, ciki har da Jagoran Addinin Iran Ali Khamenei.
Iran ta mayar da martani da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami kan Isra'ila da kuma Jordan, da Iraki da ƙasashen yankin Gulf da ke ɗauke da kadarorin sojojin Amurka.
Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanya ce ta jigilar kayayyaki a duniya, ita ma an rufe ta tun a farkon watan Maris.
A kowace rana aƙalla ganga miliyan 20 na mai ne suke wucewa ta hanyar, kuma katsewar hanyar a yanzu ya haifar da hauhawar farashin jigilar kaya da kuma ƙara farashin mai a duniya.




