Aikin layin dogo da ya haɗa arewacin Kamaru da babban birnin Chadi N'Djamena, wanda aka fi sani da ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen haɗin gwiwar yankin Afirka ta Tsakiya, ya janyo takaddama tsakanin Yaoundé da N'Djamena.
A farkon watan Yunin nan ne hukumomin Kamaru suka amince a shimfida wata hanya da za ta ratsa Ngaoundéré, Garoua, Maroua, Kousseri da N'Djamena, sai dai a bangare guda gwamnatin Chadi ta bayyana cewa ba a yanke shawara ta ƙarshe ba tukuna inda ta yi kira da a yi zama tsakanin ƙasashen biyu kafin a tabbatar da daukar wani mataki, a cewar Tchadinfos.
A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Sufuri ta Chadi ta fitar, N'Djamena ta jaddada cewa "ana nazari kan dukka zaɓukan da ake da su" kuma ya kamata a samu zaɓin hanyar daga yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
Kamar yadda majiyoyi da dama suka rawaito, Chadi ta fi son a samar da hanyoyi a kudancin kasar wadanda za su fi anfanarwa ga manyan yankunan noma da tattalin arziki a ƙasar, a wani mataki na ƙarfafa haɗin kai na cikin gida da kuma ƙara fa'idodin tattalin arziki na gaba a hanyoyin jiragen ƙasa.
Hanyar da Yaoundé ta bayar ta samu amince wa a hukumance daga fadar shugaban ƙasar Kamaru a ranar 5 ga Yuni. Yana ɗaya daga cikin wani ɓangaren aikin layin dogo da ya kai kusan kilomita 1,000, inda aka yi hasashen za a kashe tsakanin kuɗin CFA triliyan 4 zuwa 6 ko da yake ya danganta da binciken da aka yi nazari a kai.
Da farko an mayar da hankali kan hanyoyi uku kafin daga baya Kamaru ta zaɓi hanyar da za ta ratsa manyan biranen yankin Arewa Mai Nisa, in ji Tchadinfos.
Babban matakin sulhu
Baya ga takaddamar da ake yi kan batun hanyar layin dogon, aikin yana da matukar mahimmanci, musamman ga Chadi, ƙasar da ba ta da ruwa, ba ta da hanyar shiga teku kai tsaye da kuma na wadda za ta haɗa jirgin ƙasa,
Hanyar jirgin ƙasar za ta samar da wata muhimmiyar mahaɗa zuwa Tashar Jiragen Ruwa ta Douala ta hanyar tsarin jirgin ƙasa na Kamaru.
Ana sa ran layin dogo zai rage farashin sufuri, inganta zirga-zirgar kayayyaki, da kuma haɓaka ciniki da musayar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu maƙwabta.
A ɓangaren Kamaru kuma, layin dogo zai ƙarfafa rawar da take takawa a matsayin babbar hanyar sufuri ta yankin Afirka ta Tsakiya kuma za ta ƙarfafa matsayinta na babbar hanyar sufuri ta kayayyakin abinci da za a shiga Chadi da yankunan Sahel mai faɗi.
Kazalika, ana ganin wannan aikin a matsayin wannan za ta sama da ci gaban tattalin arziki da kwanciyar hankali a yankunan arewacin ƙasar, waɗanda ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro da matsalar zamantakewa da ta tattalin arziki.














