NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin kwanon abinci a filin jirgin saman Legas

Ya bayyana cewa ƙarin bincike ya nuna cewa Agoro Moninuol, wani mai tura kayyayki ƙasashen waje mai shekara 52 ne ya tura kayayyakin.

By
TSOHON HOTO: Kusan kowane mako hukumar NDLEA na bayar da rohotannin kama masu safarar ƙwayoyi / NDLEA

Jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA sun kama hodar iblis da tabar wiwi da aka ɓoye cikin kwanon abinci a filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Hukumar ta ce an kama tabar wiwi da nauyinta ya kai kilo 2.80 a cikin kwanuka masu riƙe zafin abinci da aka fi sani flask waɗanda za a kai Birtaniya ta jirgin sama na Virgin Atlantic a filin jiragen sama na Murtala Muhammed na Legas.

Wata sanawar da mai maganada yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi ta ce an yi kamen ne a ranar Alhamis 9 ga watan Afrilu ta shekarar 2026, a ofishin fitar da kayayyaki na filin jiragen saman, lamarin da ya sa aka kama ma’aikatan jigilar kaya biyu, Ama Obinna Ufeim ( mai shekara33) da Ogabi Monday Akorede (mai shekara 39).

Ya bayyana cewa ƙarin bincike ya nuna cewa Agoro Moninuola, wani mai tura kayyayaki ƙasashen waje mai shekara 52 ne ya tura kayayyakin.

Sanarwar ta ce, “Jami’ai sun kama jerin manyan ƙullin hodar iblis masu yawa da aka ɓoye a ƙasan abinci na bogi a kwanukan, wadanda aka dauka da niyyar kai su Birtaniya daga filin jiragen sama na Murtala Muhammed a Ikeja, Legas.