Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi alhinin rasuwar Dr. Adam Ibrahim Ismail, wanda aka kashe a Al Fasher; tana mai kira da a dinga bai wa ma'aikatan lafiya kariya.

By
Tedros ya ce "zaman lafiya shi ne maganin da ya fi kowanne karfi."

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta yi kira da a kawo karshen yakin Sudan bayan da aka kashe wani likita a yankin Al Fasher da rikicin ya fi kamari.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya rubuta a shafin X a ranar Lahadi cewa |Dole a kawo karshen zubar da jini a Sudan.”

Ya ce ya yi “bakin ciki matuka da samun labarin kisan Dr Adam Ibrahim a wani rikicin a yankin Al Fasher na Sudan,” yana mai cewa “WHO ta yi alhinin mutuwar Dr Ismail tare da neman kawo karshen kisan da ake yi wa jami’an lafiya.

Tedros ya kammala sakon nasa da rokon samar da zaman lafiya, yana mai cewa: “Zaman lafiya shi ne maganin da ya fi kowanne karfi.”

A ranar 26 ga watan Oktoba ne mayakan ‘yan-aware na RSF suka kwace iko da Al Fasher suke kuma aikata kisan kiyashi, kamar yadda hukumomin kasa da na duniya ke fada, inda ake gargadin cewa cin zalin da ake yi zai iya shiga wasu yankunan da dama.

Tun watan Afrilun 2023, rundunar sojin Sudan da mayakn RSF suke fafata yakin da ya yi ajalin dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.