Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana wata ajanda mai cike da buri na faɗaɗa muhimmiyar dangantakar Turkiyya da Koriya ta Kudu, inda ya ayyana wata manufa ta cinikayyar dala biliyan $15 da kuma bayyana makamashin nukiliya da masana’antar tsaro da fasaha mai zurfi da ababen more rayuwa na sufuri a matsayin muhimman fannonin haɗin kai.
A wata hira da kamfanin dillancin labaran Koriya ta Kudu Yonhap gabanin ziyararsa ta ƙasa zuwa Seoul, Erdogan ya ce ya kamata ƙasashen biyu su ƙara gini kan dangantakarsu mai cike da tarihi, da ke da asali a yaƙin Koriya, su kuma sauya ƙwancensu daɗaɗɗe zuwa dangantaka ta tattalin arziki da fasaha mai ƙarfi.
Ziyarar na zuwa ne gabanin bikin tunawa da shekara ta 70 ta hulɗar diflomasiyya tsakanin Turkiyya da Koriya ta Kudu a shekara mai zuwa. Erdogan ya ce ƙarfafa tattaunawar siyasa da ƙara zuba jari da kuma faɗaɗa haɗin kai na masana’antu za su kasance mafi muhimmanci batutuwa a tattaunawar.
Tattaunawa zai mayar da hankali kan makamashin nukiliya da cinikayya
Erdogan ya bayyana Koriya ta Kudu a matsayar ƙsar da za ta kasance babbar abokiyar hulɗa wajen gina tashar makamashi ta nukiliya Sinop da Turkiyya ke shirin ginawa, yana mai cewa tattaunawa da ɓangaren Koriya ya yi gababiyo bayan yarjejeniyar fahimtar juna da aka sanya wa hannu a shekarar da ta gabata.
Turkiyya ta kuma gudanar da aiki na bincike na yiwuwar aiki da kamfanin makamshin Koriya (KEPCO), yayin da tantancewa ke ci gaba game da yanayi na fasaha da tattalin arziki da kuma tsarin zuba jari na aikin.
Shugaban ya ce shawarar da za yanke a ƙarshe zai dangana ne game da tsadar samar da lantarki da tsarin samar da kuɗi da kuma fa’idar aikin gabaɗaya ga tattalin arzikin Turkiyya.
Game da cinikayya, ya yi ishara ga muhimmin rashin daidaito tsakanin ƙasashen biyu. Turkiyya ta fitar da kayayyaki da kimarsu ta kimanin dala biliyan $1.14 zuna Koriya ta Kudu a shekarar 2025, yayin da kimar kayayyakin da ta shigo da su ya kai dala biliyan $10.26.
Erdogan ya ceAnkara na son ta rage wannan giɓin ta kuma mayar da cinikayyar mai ƙrin daidaito da kuma ɗorewa, da damarmaki na zuba jari ga Koriya a fannonin ƙera motoci da batura da semiconductors da mutummutumi da fasahar halittu da kayayyakin aikin jinya da makamashin da ake iya sabuntawa.
Ya yi ishara ga ayyukan ƙra mota na kamfanin Hyundai da na zuba jari a harkar ƙarafa’ na kamfanin POSCO a Turkiyya a matsayin misalan haɗin kai da ke tafiya halin yanzu, yana mai ƙarawa da cewa ƙaddamar da aikin ƙera motoci na laturoni a masana’antar Hyundai da ke Izmit abin maraba ne.
Hadin kai na tsaro na ƙara ƙarfi
Shugaban na Turkiyya ya kuma bayyana damarmaki na faɗaɗa haɗin kai na masana’antar tsaro, musamman game da jirage mara matuƙa da kuma fasaha na inji.
Ya yi maraba da rahoton da ke cewa Koriya ta Kudu na son inji samfurin PD170, wanda ƙirar kamfanin ƙera ijuna na Turkiyya (TEI), wani ɓangare na rukumomin kamfanin ƙera jiragen saman Turkiyya. Ana amfani da injin ɗin ne a jirage mara matuƙan Turkiyya samfurin ANKA da AKSUNGUR.
Erdogan ya bayyana son injin ɗin a matsayin wani abu da ya nuna ci-gaba da injiniyoyin Turkiyya suka ta samu kuma ya ce ƙasashen biyu za su iya faɗaɗa haɗin kai da suke da shi a fannin tsaro zuwa tsarin mara matuƙ da injuna da tsare-tsaren laturoni da aikin injiniya mai zurfi.
Ya kuma yi ishara ga babbar tankar yaƙi ta Altay a matsayin wani misali na haɗin kai na baya da ƙasashen suka yi a fannin tsaro.
Erdogan ya yi kira da taka rawa na bai ɗaya a aikin sake gina Gaza
Da ya mayar da hankali ga TGaza, Erdogan ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta wani muhimmin mataki ne amma bai dawo da rayuwa yadda yake da ba ga Falasɗinawa, waɗanda suka ci gaba da fuskantar matsancin yanayi na jinƙai.
Ya nemi a cire ababen da hana isar da kayayyakin agaji da gaggauta sake gina yankin, yana mai jaddada buƙatar da ke akwai na sake gina asibitoci da makaranti da gidaje da kuma dawo da ababen more rayuwa na ruwa da lantarki.
Erdogan ya yi maraba da kalaman Shugaban ƙasar Korita Ta Kudu Lee Jae-myung kan Gaza da kuma goyon baya ga tallafi na jinƙai. Ya ce ƙwarewar Turkiyya a fannin ba da agaji da gine-gine da ababen more rayuwa za su iya taimaka wa ƙarfin Koriya a fannin fasaha da jinjiniya da samar da kuɗi.
Ƙasashen biyu za su iya haɗa kai waje sake gina asibitoci da makaranti da gidaje tare da dawo da makamashi da ruwa, in ji shi.
Duk da haka, Erdogan ya jaddada cewa dole Falasɗinawa su yanke hukunci game da makomar Gaza kuma ya yi watsi da duk wani tsari na sake gina wurin da zai tilasta musu barin ƙasaru ta gado.
Ya nanata matsayar Turkiyya cewa zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta bisa ga kan iyakoki na shekarar 1967, da gabashin Birnin Ƙudus a matsayin babbn birnin ƙasar.
Tsaron yani da hanyoyin sufuri
Erdogan also addressed tensions involving Yemen and Saudi Arabia, condemning attacks targeting civilians and airports and expressing Türkiye’s support for Saudi Arabia’s sovereignty, territorial integrity and security.
He said Ankara was working to advance the Mecca Agreement, including through its approval process in the Turkish parliament and efforts to strengthen institutional cooperation and joint defence capabilities.
On Yemen, Erdogan called for an end to the fighting and a political settlement involving all parties, while emphasising the need to preserve the country’s sovereignty and territorial integrity.
The president also highlighted the strategic importance of Türkiye’s transport links as disruptions affect shipping through the Strait of Hormuz and the Bab al Mandab.
He said the risks to global energy and trade routes underscored the need for reliable alternative corridors, pointing to Türkiye’s efforts to connect railways, roads, ports and logistics centres into an integrated transport network.
Among the projects he outlined was the revival of the historic Hejaz Railway, built during the reign of Ottoman Sultan Abdulhamid II. Türkiye is pursuing work with Syria and Jordan, while agreements with Saudi Arabia on railway and logistics cooperation are also part of the wider effort to strengthen connections between the Gulf, Türkiye and Europe.
Erdogan additionally cited the Middle Corridor, which crosses the Caspian Sea, and the Development Road project linking Iraq’s Grand Faw Port to Türkiye as complementary routes that could expand regional trade and reduce transport times and costs.
He said South Korean companies could contribute through railway infrastructure, signalling, communications systems, logistics centres and intelligent transport technologies, adding that Ankara was ready to support Korean firms investing and creating jobs in Türkiye.



















