Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta sanar da tsanant sa ido tare da tsananta bincike a ɗaukacin iyakokin ƙasar da filayen jiragen sama domin hana cutar shiga cikin ƙasar.
Babban Daraktan Hukumar ta NCDC Jide Idris wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ya ce hukumar tana ƙara sanya ɗakunan bincike cikin shirin ko-ta-kwana, da shirin hana yaɗuwar cutar, da wayar da kan jama’a a duka fadin ƙasar.
NCDC ta ɗauki matakin ne bayan Hukuma Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana ɓarkewar annobar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DRC) da kuma maƙwabciyarta Uganda a matsayin "babbar matsala ta lafiya da ta shafi duniya baki ɗaya."
Matakin ya biyo bayan rahoton mutuwar mutane akalla 88 da kuma wasu sama da 300 da ake zargin sun kamu da cutar.
Babban Daraktan WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, shi ne ya sanar da wannan matakin na gaggawa. Cutar, wacce ta fara ɓulla a lardin Ituri da ke gabashin Congo, ta bazu cikin sauri inda har aka tabbatar da samun masu ɗauke da ita a birnin Kampala na ƙasar Uganda.
Matakan da Nijeriya ta ɗauka na ko-ta-kwana
Yayin da take tabbatar wa 'yan ƙasar cewa kawo yanzu ba a sami mutum ko ɗaya da ya kamu da cutar ba a Nijeriya, hukumar NCDC ta ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba saboda yawan zirga-zirgar mutane tsakanin kasashen Afirka.
Babban Daraktan NCDC, Dr. Jide Idris, ya ba da umarni na gaggawa ga ɗaukacin kwamishononin lafiya na jihohin ƙasar da su gaggauta farfaɗo da cibiyoyin agajin gaggawa na kiwon lafiya.
Shirin ya ƙunshi, sanya iyakoki cikin shiri ta hanyar tsananta binciken lafiyar matafiya a dukkan filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa, da iyakokin ƙasa, da gaɓar teku.
Haka ya yi umarnin tura kayan aiki da na bincike don tabbatar da cewa ma'aikatan lafiya suna da kayan kariya na musamman da na'urorin auna zafin jiki
Haka kuma shugaban na NCDC ya umarci jihohi da su tanadi wuraren killace marasa lafiya da kuma shirya dabarun binne mamata cikin amintacciyar hanya, duba da cewa gawawwakin waɗanda Ebola ta kashe na da matukar haɗarin yaɗa cutar.
Hukumar ta NCDC ta yi kira ga al'ummar Nijeriya da su kwantar da hankulansu, su guji yada jita-jita, sannan su kiyaye wadannan matakai na kare kai
Matakan sun haɗa da wanke hannaye akai-akai da ruwa da sabulu, da guje wa taɓa jini, amai, gumi, ko sauran ruwan jikin mutumin da ke nuna alamun rashin lafiya, da guje wa cin naman daji ko taɓa matattun dabbobi da ba a san sanadin mutuwarsu ba, da kuma kai rahoton duk wani mutum da ke nuna alamun zazzabi mai tsanani, ciwon kai, amai, ko zubar jini ta hanyoyin jiki zuwa asibiti mafi kusa, musamman idan mutumin yana da tarihin tafiya ƙasashen da abin ya shafa.












