| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
Shugaba Paul Biya ya koma Kamaru bayan ya shafe kwanaki 73 ba ya nan
Shugaba Paul Biya ya koma Kamaru bayan ya shafe kwanaki  73 ba ya nan
Shugaban Kamaru Paul Biya

Shugaba Paul Biya ya koma Kamaru a ranar Alhamis bayan hutun kwanaki 73 lamarin ya haifar da jita-jita game da lafiyar tsohon shugaban mai shekaru 93 wanda ke jagorantar ƙasar.

Shugaba mafi tsufa a duniya, Biya ya sauka a Yaounde da misalin karfe 4:00 agogon GMT daga Geneva, inda ya zauna tun ranar 7 ga Yuni kan abin da ofishinsa ya kira "zama na sirri na ɗan gajeren lokaci".

Kafafen watsa labarai na Kamaru sun ruwaito cewa Biya, wanda ya kasance shugaban ƙasar tun shekarar 1982, yana Switzerland tare da 'yan’uwa da mataimaka na kud-da-kud.

Bayan fiye da watanni biyu da ya yi tafiya, shugaban ya bar filin jirgin sama tare da uwargidansa Chantal Biya, suna ɗaga hannu daga mota a kan hanyarsa ta zuwa fadar shugaban kasa.

Magoya bayan jam'iyya mai mulki da dama sun taru a filin jirgin sama don yi masa maraba da gida, wasu suna sanye da tufafi masu ɗauke da hoton Biya.

An daɗe ana jita-jita kan lafiyar Biya, wanda galibi ana cewa ya fi zama a Geneva.

A ranar 18 ga Yuni, Ministan Sadarwa Rene Emmanuel Sadi ya musanta rahotannin cewa an kwantar da Biya a wani asibiti a Geneva.