Amurka ta ce China na shirin kai wa Iran makaman kare sararin samaniya – Rahoto

Wani rahoton kafar watsa labarai ta CNN ya ambato majiyoyi da ba a bayyana sunansu ba da kuma rahoton binciken sirri, wanda ya ce China na shirye-shiryen tura wa Iran wasu nau’ukan makamai masu linzami da ake harba su daga kafaɗa.

By
Ginin Ma'aikatar Yaƙin Amurka Pentagon da ke Arlington, Virginia, wanda aka ɗauki hotonsa ranar 9 ga Oktoban 2020. / Reuters

Hukumar leƙen asiri ta Amurka ta nuna cewa China tana shirye-shiryen isar da sabbin makaman kariya daga hare-haren sama ga ƙasar Iran a ’yan makwanni masu zuwa, kamar yadda CNN ta ruwaito a ranar Juma’a, tana mai ambatar mutane uku da suke da masaniya kan lamarin.

CNN ta ce akwai alamu da ke nuna cewa China na ƙoƙarin tura kayayyakin ta wasu ƙasashe na daban domin ɓoye asalin inda makaman suka fito.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da Fadar White House da kuma ofishin jakadancin China da ke birnin Washington ba su mayar da martani ba dangane da buƙatar jin ta bakinsu da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nema.


CNN ta bayyana cewa China tana shirye-shiryen tura makaman kariya daga hare-haren jiragen sama da ake ɗora su a kafaɗa waɗanda aka sani da MANPADs, tana mai ambatar majiyoyin da ba ta bayyana sunansu ba.

Gwamnatocin Amurka da Iran na shirin gudanar da wata babbar tattaunawa a ranar Asabar a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan, da nufin lalubo hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin da suka kwashe makwanni shida suna fafatawa.