Bam da aka binne a titi ya halaka mutane a Jihar Zamfara, wasu da dama sun jikkata
Rundunar 'yansandan Zamfara ta tabbatar da fashewar bam ɗin a ranar Asabar, sai dai ba ta yi ƙarin bayani kan yawan mutanen da suka mutu da waɗanda suka jikkata ba. Amma kafofin watsa labaran kasar suna rawaito cewa aƙalla mutum 7 ne suka mutu.
Akalla mutum bakawai ne suka mutu yayin da wani bam ya tashi a kan hanyar Magami zuwa Dansadau a Jihar Zamfara da ke arewacin Njeriya a ranar Asabar.
Rundunar ‘yansandan jihar ta tabbatar da fashewar bam ɗin a ranar Asabar da rana, sai dai ba ta yi ƙarin bayani kan yawan mutanen da suka mutu da waɗanda suka jikkata ba. Amma kafofin watsa labaran kasar suna rawaito cewa aƙalla mutum 7 ne suka mutu.
Sanarwar da kakakin rundunar DSP Yazid Abubakar ya sanya wa hannu ta ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Maikogo da ke karamar hukumar Maru, a jihar ta Zamfara da misalin 2:30 na ranar Asabar.
DSP Yazid ya ce bam ɗin wanda ba a san wanda ya dasa shi ba ya yi kaca-kaca da wata tirela, har ma ba a iya tantance motar, “kuma ya yi sanadin mutuwar mutane, ciki har da wani mai babur da yake daidai wajen lokacin da lamarin ya faru.”
Sai dai ya ce har lokacin yake fitar da sanarwar babu takamaimen alƙaluma kan yawan wadanda suka mutu. Ya kara da cewa tuni rundunar ta kaddamar da bincike kan lamarin.
Kakkin gwamnan jihar Mustapha Kaura ya shaida wa manema labarai na kasar cewa ‘yanbindiga ne suka kai harin wadanda suke tserewa daga dabar wani babban jagoransu da ya yi kaurin suna, saboda hare-haren da aka kai musu.