AFCON ta cancanci girmamawa daidai da Kofin Duniya, in ji Chukwueze
Mun je an saka AFCON 2025 a lokacin da bai dace ba, amma a ce ba shi da gasa ce mai girma ba, ba abin da za a karɓa ne, in ji Samuel Chukwueze na Nijeriya.
Ɗanwasan gaban tawagar Nijeriya, Samuel Chukwueze ya yi imani cewa ya kamata a bai wa gasar kofin nahiyar Afirka (AFCON) daraja irin ɗaya da ta Gasar Kofin Duniya da Gasar Kofin Turai.
Chukwueze ya yi maganar nan ne bayan cecekuce da ake yi kan lokacin gudanar da gasar da ake yi yanzu a Maroko.
Tun da fari an shirya gasar ta wannan shekara a lokacin bazara, amma sai aka mayar da ita daga 21 ga Disambar 2025 zuwa 18 ga Janairu 2026, abin da ya hana manyan kulob-kulob na Turai samun 'yan wasa masu muhimmanci a wani muhimmin mataki na kakar wasanni ta cikin gida.
'Kowa na son ya buga AFCON. Ita ɗaya ce cikin kyawawan gasanni a duniya,' Chukwueze ya shaida wa On Sports TV.
“Dole ne a girmama AFCON yadda ake girmama Gasar Kofin Turai ko Gasar Kofin Duniya.'
“Mun fahimci cewa an shirya ta a lokacin da bai dace ba a shekara, amma tun da gasa ce mai muhimmanci, idan an kira ka dole ne ka je,' in ji shi.
“Ba ka da wani zaɓi, kulob ɗinka ba zai iya hana ka ba kuma babu wanda ya kamata ya ce wani abu mara kyau game da AFCON. E, sun sa ta a lokacin da bai dace ba, amma cewa ba gasa ce mai kyau ko ba babbar gasar ba ce, ba abin karɓa ba ne.”
Chukwueze ya taimaka wa Nijeriya samun nasara a wasansu na farko da ci 2-1 kan Tanzania a Rukunin C. Wasansu na gaba za su buga da Tunisia ranar Asabar.