Dakarun Isra'ila sun ƙwace kayayyakin tarihi biyar a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye

Rundunar sojin Isra''ila ta kai samame wani wuri mai tsaunuka kuma ta ƙwace wasu ginshiƙai na lokacin Daular Rumawa, kamar yadda wasu ganau suka bayyana.

By
Ragowar kayan tarihi a wajen binciken tarihi na Sebastia, yammacin Nablus a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye ranar 30, ga Nuwamban 2025 / AFP

Dakarun Isra’ila sun ƙwace kayayyakin tarihi guda biyara ranar Alhamis a garin Al-Mazra'a ash-Sharqiya, da ke arewa maso gabashin Ramallah a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, in ji wasu da suka gane wa idonsa lamarin.

Rundunar sojin isra’ila, tare da rakiyar wakilai daga hukumomin farar hula na Isra’ila , sun kai samame wani yanki mai tsaunuka cikin garin kuma sun ƙwace ginshiƙai biyar na zamanin Daular Rumawa a wani wurin binciken kayan tarihi, a cewar shaidun gani da ido.

Rahotannin kafafn watsa labaran Isra’ila na baya bayan nan sun yi iƙirarin cewa an ƙwace ginshiƙan ne bisa zarge-zargen cewa Falasɗinawa na gine-gine a wurin kuma suna lalata kayayyakin tarihi.

Minsitan yawon buɗe ido da tarihi na Falasɗinawa Hani al-Hayek ya ce hare-haren Isra’ila sun lalata gaɓa ɗaya ko kuma wani ɓangare na wuraren binciken tarihi da wuraren tarihi 316, yana mai bayyana cewa hare-haren sun kasance "laifukan yaƙi da aka yi domin shafe tarihin Falasɗinawa."

Muayyad Shaban, Shugaban Hukumar Tirjiya kan Gina Katanga da Tsugunar da Mutane na Ƙungiyar Gwagwarmayar Falasɗinawa ta PLO, tun da farko ya bayyana cewa Isra’ila tana shirin ƙwace fili da ya kai dunam 4,600 dunams ( kadada 1,137 ko kuma acres 1,137) a garuruwan Sebastia da Burqa kusa da Nablus a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da sunan kare wuraren tairhi.