An buƙaci Nijeriya ta gyara yadda ake bayar da labaran rikice-rikice

An cim ma wannan matsaya ne a wajen wani babban yaro a Abuja da Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Ƙasa ta ɗauki nauyin gudanarwa tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro.

By
Gwamnatin Nijeriya ta ce yana da matuƙar muhimmanci a riƙa yin kaffa-kaffa wajen amfani da wasu kalamai a yayin bayar da labarai kan rikice-rikice / User Upload

Masu ruwa da tsaki a fannin tsaro da kafofin watsa labarai da ƙungiyoyin farar-hula a Nijeriya sun yi kiran gaggawa kan yin kwaskwarima ga yadda ake rawaito labaran rikice-rikice, suna gargaɗin cewa kalamai na rashin kula na ta’azzara rashin tsaro da barazana ga zaman lafiya tsakanin ‘yan ƙasar.

An cim ma wannan matsaya ce a wajen wani babban yaro a Abuja da Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa ta ɗauki nauyin gudanarwa tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Bawa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro da Shirin UKAid.

Mahalarta taron da suka haɗa da ‘yanjarida, malaman jami’a, jami’an soji, da shugabannin addini - sun amince da cewa Nijeriya ba yaƙi a fagen fama kawai take fama da shi ba, har ma da na yadda ake bayar da labaran da yadda jama’a ke fahimtarsu.

A jawabin buɗe taron, Ministan Watsa Labarai da Wayar da Kan Jama’a Mohammed Idris ya ce “kalmomi abin dubawa ne”, musamman a al’ummar da ke da ƙalubale.

Ya yi gargaɗin cewa rashin zaɓar kalmomi masu kyau na iya ingiza rikici, ƙarfafa kallo-kallo ga juna da kawar da amincewa juna tsakanin ‘yan ƙasa da hukumomi.

Ya ƙara da cewa bayanai marasa kan gado game da rikici musamman wanda ya shafi ƙabilanci ko addini, da ma ƙasƙantar da manyan laifuka da rikicin filaye da gazawar shugabanci, waɗanda aka bayyana su ta kafafen watsa labarai na iya raba kawunan al’umma.

Ma’aikatan watsa labarai da suka halarci taron sun bayyana matsin lambar da suke fuskanta ta bayar da labari nan da nan, wanda hanzarin na janyo matsalar daidai da ingancin labaran.

Jami’an tsaro su ma da suka halarci taron sun bayyana hatsarin da ke tattare da labaran da ba a tabbatar da ingancinsu ba, waɗanda za su iya cin karo da gaskiyar abin da ya faru.

Babban Jami’in Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci, Adamu Garba Laka, ya ce harshe ba kawai batu ne na sadarwa ba, har ma da yadda al’amura ke gudana, kuma siffanta jama’a yadda aka ga dama na iya raunana tattara bayanan sirri.

Ya yi gargaɗi kan nuna wata al’umma gaba ɗaya ba ta kyau tare da kira sa a ɗauki matakan gyara hakan.

Jakadan Angola a Nijeriya, Jose Bamokina Zau, ya yi gargaɗin cewa yadda ake fayyace rikici ne tabbatar da yadda za a magance shi.

Shi ma jakadan Rwanda a Abuja, Moses Rugema ya bayar da misalan irin abubuwan da suka afku a Rwanda yayin kisan kiyashi, yana mai bayyana yadda zuzuta kalamai da tsangamar wata ƙabila ke ba da gudunmawa wajen rikita al’amura a ƙasa.

Babban sakamakon taron na Abuja shi ne a lalubo hanyoyin da za a magance yadda ake bayar sa labaran rikice-rikice a ƙasar.