Mata manya da yaransu a jihar Rakhine ta kasar Myammar na fuskantar tsanantar fyade a yankunan da ke karkashin ikon Sojojin Arakan (AA), kamar yadda wani rahoto na ‘Yan Burma Rohingya da ke Rayuwa a Birtaniya ya bayyana wanda aka fitar a ranar 14 ga May
A yayin da ake fuskantar rasa matsugunai da munanar yanayin jinkai, rahoton ya ce cin zarafin mata - da ma barazanar yin fyade - sun zama babban makamin yin barazana da kai wa Musulmai marasa rinjaye hari.
An dade ana amfani da cin zarafi a matsayin makami kan ‘yan Rohingya a Myammar da mabiya Budha suka fi yawa, inda suke fuskantar rikici tsawon shekaru, ciki har da a 2017 da aka yi musu kisan kiyashi.
Kusan shekaru 10 daba baya, an rasa wanda zai dauki nauyin laifin tare da kama shi, inda alummar Rohingya ke ci gaba da fuskantar cusgunawa, nuna wariya, da hana su zama ‘yan kasa da ma taye hakkokinsu da dama daga mahukuntan kasar sojoji.
Cin zarafin mata a lokutan yaki ya saba wa dokokin kasa da kasa na jinkai kuma na iya zama babban laifi ga bil’adama, laifukan yaki da ayyukan kisan kiyashi.





