Hedkwatar sojin Nijeriya ta ce an kashe wasu dakarunta a wani hari da ‘yanta’addan Boko Haram suka kai a hedkwatarsu da ke Benisheikh a Jihar Borno, arewa maso gabashin ƙasar.
Wata sanarwa da daraktan watsa labarai na hedkwatar tsaron Nijeriya Manjo Janar Michael Onoja ya fitar ranar Alhamis ta ce ‘yanta’addan sun yi yunƙurin kutsawa cikin hedkwatar da misalin ƙarfe 12:30 na dare amma dakarun ƙasar sun daƙile su.
Ya ƙara da cewa dakarun na Nijeriya, waɗanda kwamandansu Birgediya Janar Oseni Braimah ya jagoranta, sun “mayar da martani bisa jajircewa da ƙwarewa da kuma ƙarfin da ya fi na maharan,” abin da ya tilasta musu ja da baya.
Manjo Janar Onoja ya ce “abin takaici shi ne, gumurzun ya yi sanadin rasa wasu jajirtattun sojoji waɗanda suka mutu a lokacin aiki.”
Ko da yake kakakin hedkwatar tsaron ta Nijeriya bai bayyana yawan sojojin da suka mutu ba, amma wasu rahotanni sun ce dakaru da dama sun rasu cikinsu har da Birgediya Janar Braimah.
Nijeriya, mafi yawan al’umma a Afirka, ta daɗe tana fama da rashin tsaro, musamman a arewacin ƙasar inda aka kwashe shekaru da dama ana fuskantar hare-haren ‘yanta’addan Boko Haram da ISWAP da masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.












