Hukumar Kwastam ta Nijeriya da Gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun yarjejeniya ta dabarun tsaron kan iyaka, kare kayayyakin da ke wucewa ta iyakoki da kuma bunƙasa hulɗar tattalin arziƙi.
Babban Kwanturola Janar na hukumar kwastam na Nijeriya Bashir Adeniyi, ne ya bayyana hakan a wani babban taron tattaunawar haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kwastam ta Nijeriya da Hukumar Kwastam ta Jamhuriyar Nijar da aka gudanar a Abuja. Tawagar Nijar ta samu jagorancin Darakta Janar ɗinta, Muhammadu Yaqouba.
Adeniyi ya ce haɗin gwiwar za ta mayar da hankali ne kan sauƙaƙa kasuwancin yankin, kare kayayyakin da ke wucewa, ƙarfafa musayar bayanai, da inganta haɗin gwiwar tsaro a kan iyaka.
A cewarsa, an tsara wannan haɗin gwiwa ne domin inganta jigilar kayayyakin da ake kaiwa Jamhuriyar Nijar ta hanyar Nijeriya, magance matsalolin tsaro a kan iyakokin ƙasashen biyu, da rage jinkiri a manyan hanyoyin wucewar kayayyaki, domin tabbatar da cewa halastaccen kasuwanci yana ba da gudunmawa yadda ya kamata ga bunƙasar tattalin arziƙin ƙasashen biyu.
Babban Kwanturola Janar ɗin ya amince cewa ƙasashen da ba su da tashar ruwa suna fuskantar ƙalubale wajen gudanar da ayyuka, yana mai cewa dogaro da tashoshin jiragen ruwa da kayayyakin more rayuwa na maƙwabtan ƙasashe na ƙara tsadar harkokin kasuwanci tare da rage gasa.
Ya ƙara da cewa, “Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta daɗe tana taimaka wa maƙwabtanmu da ba su da tashar ruwa, ciki har da Jamhuriyar Nijar, wajen sauƙaƙa harkokin kasuwanci. Wannan ƙuduri zai ci gaba duk da bambance-bambancen siyasa, domin kasuwanci, tsaro, da zaman lafiyar yankin suna da alaƙa da juna.”
Da yake magana kan matsalolin da ake fuskanta wajen jigilar kayayyakin da ke wucewa, Adeniyi ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da kafa hanyoyin tsaro na musamman da kuma samar da izinin wucewa cikin aminci domin sauƙaƙa zirga-zirgar manyan motoci masu ɗauke da kaya da ke jiran tantancewa.
















