Rundunar ‘yansandan jihar Kaduna ta ce ta kama mutane da dama bisa zarginsu da hannu a kisan gillar da wani gungun mutane ya yi wa wata mata bisa zargin satar yara.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mandir Hassan, ya fitar ta ce lamarin ya auku ne a yankin Mararrabar Jos a ranar 21 ga watan Yunin shekarar 2026.
Rundunar ta ce an yi ƙoƙarin ceto matar da lamarin ya shafa, kuma an kai ta ofishin ‘yansanda domin tsaronta da kuma bincike.
“Sai dai, ɗaruruwan fusatattun mutane sun danna ofishin ‘yansandan kuma suka yi wa ofishin ƙawanya, sannan suka nuna wa ‘yansandan da ke aiki fin-ƙarfi inda suka ƙwato matar da ƙarfin tuwo kuma suka kashe ta tare da ƙona gawarta,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa matar da lamarin ya rutsa da ita ‘yar garin Mararrabar Jos ce.
Rundunar ta bayyana wannan aika-aikar a matsayin aikin jahilci da laifi da kuma hari kai-tsaye ga tsarin biyayya ga doka.
Babu wani mutum ko kuma wata ƙungiya da ke da iko na ɗaukar doka a hannunsu, in ji rundunar ‘yansandan.
Rundunar ta kuma Allah wadai da lamarin, inda ta sha alwashin gurfanar da duk wanda aka samu da hann a aika-aikar.
An fara cikakken bincike, kuma dukkan waɗanda ke da laifi za su fuskanci cikaken hukuncin doka, a cewar sanarwar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Rabiu Muhammad, ya yi gargaɗin cewa rundunar ‘yansandan jihar ba za ta lamunci ɗaukar doka a hannu ko hare-hare kan ofisoshin ‘yansanda da jami’an ‘yansanda ba.
Ya yi kira ga ‘yanƙasa su ba da bayanai kan mutane da ba su yarda da su ba ga ‘yansanda kuma su bari a bi tsari yadda ya dace.















