| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
INEC ta wallafa sunan Pantami a shafinta na ’yantakarar gwamna amma babu Gwarzo na Kano
A cikin jerin sunayen ’yan takarar da aka wallafa, an ga rubutun “Court Order” a gaban sunan jam’iyyar NDC, ba tare da bayyana sunan ɗan takararta ba.
INEC ta wallafa sunan Pantami a shafinta na ’yantakarar gwamna amma babu Gwarzo na Kano
INEC ta wallafa sunan Pantami a shafinta na ’yantakarar gwamna amma babu Gwarzo na Kano

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta saka sunan Farfesa Isa Ali Pantami cikin sabon jerin sunayen ’yan takarar gwamna a zaɓen 2027, inda zai fafata a Jihar Gombe ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Sai dai har yanzu ba a ga sunan Aminu Abdussalam Gwarzo, ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), cikin sabon jerin sunayen da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ba.

A cikin jerin sunayen ’yan takarar da aka wallafa, an ga rubutun “Court Order” a gaban sunan jam’iyyar NDC, ba tare da bayyana sunan ɗan takararta ba.

Wata majiya daga INEC da ta buƙaci a sakaya sunanta ta shaida wa TRT Afrika Hausa cewa rubutun “Court Order” a gaban sunan jam’iyya na nufin akwai wani hukuncin kotu da ya shafi shigar da sunan ɗan takararta cikin jerin sunayen.

Majiyar ta ce idan hukuncin kotun Babbar Kotu ne ko kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara, akwai yiwuwar a sauya matakin idan jam’iyyar ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli kuma ta samu nasara.

Ta ƙara da cewa INEC za ta ci gaba da bin hukuncin da ke gabanta har sai kotu ta bayar da wani sabon umarni. Idan kuwa hukuncin Kotun Ƙoli ne, to hukumar ba za ta iya sauya matsayinta ba sai an samu wani sabon hukunci.

Korafe-korafen da INEC ta karɓa

A sanarwar da ta fitar ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, INEC ta ce ta karɓi korafe-korafe 69 daga jam’iyyun siyasa 12 a jihohi 26 dangane da ’yan takarar gwamna, inda 41 suka yi nasara, yayin da aka ƙi amincewa da 28.

Dangane da zaɓen ’yan majalisun dokokin jihohi kuwa, hukumar ta ce ta karɓi korafe-korafe 61 daga jam’iyyun siyasa 11 a jihohi 11. Ta amince da 25 daga cikinsu, yayin da ta yi watsi da 36.

Korafe-korafen sun shafi cire wasu jam’iyyun siyasa daga jerin sunayen ’yan takara, shigar da sunayen mutanen da ba sa cikin rajistar mambobin jam’iyyunsu, da kuma zargin tsayar da mutum takara a jam’iyyu fiye da ɗaya.

INEC ta ce bayan nazarin korafe-korafen, ta amince da shigar da wasu ’yan takara da jam’iyyun siyasa da aka cire a baya, tare da cire wasu sunayen da aka gano cewa an saka su ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar ta kuma ce za ta ci gaba da tabbatar da gaskiya da sahihancin tsarin zaɓe.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na INEC, Mohammed Kudu Haruna, ne ya sanya hannu kan sanarwar.