Shugaban Guinea Doumbouya ya yi alkawarin ba zai yi amfani da ofishinsa don biyan buƙatar kansa ba
An rantsar da Doumbouya a hukumance a ranar Asabar a matsayin shugaban Jamhuriyar Guinea bayan ya lashe zaben shugaban ƙasa na 28 ga Disamba da kashi 86.72 cikin 100 na kuri'u
Shugaban Guinea da aka rantsar kwanan nan, Mamadi Doumbouya, ya yi alkawarin ba za ya yi amfani da ikonsa na shugaban kasa don amfanar da kansa ba; inda ya ce 'ba zai taɓa amfani da ikon da aka ba shi don bukatun kansa ba'.
An rantsar da Doumbouya a hukumance a ranar Asabar a matsayin shugaban Jamhuriyar Guinea bayan ya lashe zaben shugaban ƙasa na 28 ga Disamba da kashi 86.72 cikin 100 na kuri'u, alamar dawowar ƙasar ga mulkin farar-hula bayan fiye da shekaru huɗu na mulkin soja.
Bikin rantsuwar ya gudana a Filin Wasa na Janar Lansana Conté a Nongo, da ke gefen birnin Conakry, tare da halartar shugabanni da dama na Afirka da manyan wakilai daga sassa daban-daban na duniya. Doumbouya zai yi wa'adin shekaru bakwai.
Shugabannin Afirka a bikin rantsuwa
Kamar yadda Sahe na 59 na Kundin Tsarin Mulkin Guinea ya tanada, Doumbouya ya yi rantsuwa gaban Kotun Kolin, wadda shugaban ta na farko Fode Bangoura ya jagoranta, ya yi alkawarin biyayya ga ƙasa da girmama doka.
Shugaban Rwanda Paul Kagame, Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye, Shugaban Mali Assimi Goita, Shugaban Gambia Adama Barrow, Shugaban Mauritaniya Mohamed Ould Ghazouani, Shugaban Gabon Brice Oligui Nguema, Shugaban Saliyo Maada Bio da Shugaban Liberia Joseph Boakai na daga cikin shugabannin Afirka da suka halarci bikin rantsuwar.
An rufe babin mulkin soja
Mataimakan shugabannin kasashe daga China, Nijeriya, Ghana da Equatorial Guinea sun halarci bikin ranstuwar, tare da manyan 'yan majalisa da jami'an gwamnati daga Côte d’Ivoire, Maroko, Togo, Guinea-Bissau da Tarayyar Komoros.
Shugabannin Kwamitin ECOWAS da Kwamitin Hukumar Tarayyar Afirka ma sun halarci taron.
Rantsuwar ranar Asabar ta tabbatar da sauyawar Doumbouya daga shugaba na soja zuwa shugaban farar-hula da aka zaba. Ya jagoranci Guinea tun Satumban 2021, lokacin da ya karɓi iko a juyin mulkin soja da ya kifar da tsohon shugaban ƙasa Alpha Condé.
An yi tsammanin canjin zai kasance na ɗan lokaci, amma ya ɗauki fiye da shekaru huɗu yayin tattaunawa da ƙungiyoyi na yankin, ciki har da Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), wadda ta kakaba takunkumi a lokuta daban-daban don matsa lamba wajen samun jadawalin zaɓen dimokuradiyya.
An gudanar da zaɓen na 28 ga Disamban 2025, a matsayin mataki na ƙarshe wajen mayar da ƙasar a kan mulkin dimokuradiyya.