Fatima Adan ta fi tuna da ambaliyar ruwa kafin ta tuna da zazzabin. A ƙarshen shekarar 1997, ruwan sama ya sauka da ƙarfi kuma cikin sauri, har wani kogi da ke gudana a lokacin damina, kusa da matsugunin iyalinta a yankin Arewa maso Gabashin Kenya, ya mamaye dukkan wuraren kiwo.
Awaki ne suka fara mutuwa. Sai raƙuma. Bayan haka, cikin 'yan kwanaki, kawunta ya kamu da matsanancin ciwon kai, wanda ya sa ya kasa buɗe idanunsa. Daga baya kuma, jini ya fara fita daga hancinsa da kuma haƙoransa, wanda babu wani maganin gargajiya da aka samu a yankin da zai iya dakatar da matsalolin.
"Mun yi zaton tsinuwa ce," in ji Fatima, wadda a yanzu ke da jikoki. "Dabbobi suna mutuwa, sannan mutane ma suka fara mutuwa. Ba mu san sauro ne ke ɗauke da cutar yana yaɗa mana ita ba."
A wannan shekarar, ruwan sama mai tsanani da ke da alaƙa da wani yanayi na El Niño mafi ƙarfi da aka taɓa samu, ya haddasa ɗaya daga cikin manyan annobar cutar zazzabin Rift Valley da aka taɓa samu a Gabashin Afirka.
A gundumar Garissa kaɗai, ƙungiyoyin sa ido kan cututtuka sun gano mutuwar mutane 170 sakamakon wata cuta mai ban mamaki da ke haddasa zubar jini, kafin daga bisani aka tabbatar da ƙwayar cutar. Masu kiwon dabbobi sun bayyana cewa sun yi asarar kusan kashi 70 cikin 100 na tumakinsu da awaki, da kuma kusan kashi 30 cikin 100 na shanunsu da raƙumansu.
Illar tattalin arziƙin ta bazu zuwa wasu yankuna: haramcin fitar da dabbobi daga yankunan da cutar ta shafa ya janyo asarar kuɗi da aka kiyasta tsakanin dalar Amurka miliyan 250 zuwa 350, bisa ga bayanan Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO).
Alamun gargadi
Kusan shekaru talatin bayan haka, alamun gargaɗi sun sake bayyana. A cikin wata sanarwar gargaɗi ta haɗin gwiwa, Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da Hukumar Haɗin Kan Gwamnatocin Cigaban Gabashin Afirka (IGAD) sun yi gargaɗin cewa halin El Niño da ake ciki a yanzu ya yi “kama da wanda aka gani a shekarun 1997 zuwa 1998”.
Ana sa ran ruwan sama mai yawa da ambaliyar ruwa za su ƙara faɗaɗa wuraren da sauro ke hayayyafa a faɗin ƙasashen Ethiopia, Kenya, Somalia, Sudan ta Kudu, Tanzania da Uganda.
Zazzabin Rift Valley wata cuta ce mai tsanani, wadda ke shafar dabbobi, ciki har da tumaki, awaki, shanu, bauna da raƙuma. Haka kuma, tana iya kama mutane. Sauro ne ke yaɗa ƙwayar cutar galibi, duk da cewa mutane na iya kamuwa da ita ta hanyar taɓa jini, nono ko wasu sassan jikin dabbobin da suka kamu da cutar kai tsaye.
Za a kara yawan Kayan aikin Hukumar FAO na hasashen farko da tallafa wa yaki da cutar zazzabin Rift Valley. za a kara yawan kayayyakin a yawancin yankunan Gabashin Afirka tsakanin watan Oktoban 2026 da Janairun 2027.
Ga iyalai irin na Adan, abin da ya faru a shekarar 1997 ba wani tarihi ne da ya wuce kawai ba. Darasi ne da ke nuna irin abin da ka iya sake faruwa a nan gaba.
Kusan kilomita dubu ɗaya a kudancin yankin Morogoro na ƙasar Tanzania, Neema Mwakalinga tana da nata mummunan abin tunawar. A shekarar 2006, lokacin da cutar zazzabin Rift Valley ta bazu a faɗin Tanzania a wani lokaci na ruwan sama mai yawa, an yi wa ƙaramin garken shanun iyalinta mummunar asara. Ba wai ƙwayar cutar kaɗai ce ta haddasa hakan ba, har ma da durƙushewar kasuwar sayar da dabbobi da ta biyo baya.
Farashin bijimi babba wanda a da ake sayarwa kan kuɗin da ya kai dalar Amurka 238, ya faɗi zuwa dala 158, yayin da fargabar kamuwa da cutar ta bazu cikin sauri fiye da yadda ita kanta cutar ke yaɗuwa.
Gwamnati ta hana zirga-zirgar dabbobi daga wani wuri zuwa wani; sayar da nono ya tsaya cak; sannan mahautan da suka saba sayen dabbobin iyalinta suka daina ɗaukar wayarta.
"Cutar ba ta shigo ƙauyenmu ba, amma yunwa ta shigo," in ji Mwakalinga. "Muna da dabbobi, amma ba mu da kuɗi. Muna da nono, amma babu wanda yake son saya."
Al’ummun da aka kebe
A lokacin wannan annoba, yawan hajojin da ake cinikayya da su a Tanzania ya ragu da kashi 37 cikin 100, kamar yadda wani bincike da aka gudanar a shekarar 2006 kan annobar cutar zazzabin Rift Valley a ƙasar ya nuna.
A ƙetaren iyaka a Kenya kuwa, asarar kai tsaye da masu kiwon dabbobi suka yi ta kai kusan dalar Amurka miliyan 9.3, yayin da asarar kuɗaɗen shiga daga sayar da nono ta haura dala 77,000, bisa ga wani rahoto da mujallar Public Library of Science (PLOS) ta wallafa.
Hukumar Lafiyar Dabbobi ta Duniya (WOAH) tana ba da shawarar a sanya dokar hana fitar da dabbobi zuwa ƙasashen waje na tsawon shekaru uku bayan barkewar annoba. Irin wannan mataki na iya durƙusar da tattalin arziƙin al'ummomi makiyaya, ko da bayan sauro ya daina yaɗa cutar.
Abin da ke ƙara damun masana a yanzu ba wai girman ruwan sama da ake sa ran samu kaɗai ba ne, har ma da saurin da ambaliyar za ta iya mamaye hanyoyin kariya da yankin ke da su.
Sanarwar gargaɗin haɗin gwiwa ta FAO da IGAD ta yi kira ga ƙasashen da abin ya shafa da su ƙarfafa sa ido kan cututtuka bisa la'akari da haɗarin kamuwa da su, su tanadi alluran rigakafi tun da wuri, sannan su ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sassa daban-daban da kuma ƙasashe makwabta ta hanyar amfani da tsarin One Health (Lafiya Guda).
Sai dai kuma, irin ambaliyar ruwan da ke samar da wuraren hayayyafar sauro na iya lalata hanyoyi, kawo cikas ga ayyukan likitocin dabbobi, tare da katse hulɗa da al'ummomin da suka fi fuskantar haɗarin kamuwa da cutar.
‘Za mu iya kubutar da kawunanmu’
"Mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa da ke da alaƙa da yanayin El Niño suna taimakawa wajen yaɗuwar cutar zazzabin Rift Valley (RVF), ta hanyar faɗaɗa wuraren da sauro ke hayayyafa, tare da yiwuwar kawo cikas ga ayyukan kiwon lafiyar dabbobi," in ji FAO da IGAD a cikin sanarwar gargaɗin ta haɗin gwiwa da suka fitar.
Sauro ne ke yaɗa ƙwayar cutar galibi, amma mutane ma na iya kamuwa da ita ta hanyar taɓa dabbobin da suka kamu da cutar kai tsaye, ko kuma ta hanyar mu'amala da jininsu, nononsu ko sauran sassan jikinsu.
Annobar shekarun 1997 zuwa 1998 ta shafi kimanin mutane 89,000 a Kenya, Somalia da Tanzania, inda aka tabbatar da mutuwar mutane 478.
Haka kuma, annobar shekarun 2000 zuwa 2001, wadda ta bazu zuwa Saudiyya da Yemen, ita ce annobar farko da aka tabbatar ta faru a wajen nahiyar Afirka. Ta yi sanadin rashin lafiyar fiye da mutane 1,500, tare da mutuwar aƙalla mutum 215.
Waɗannan abubuwan da suka faru a baya sun sa gargaɗin da ake yi a yanzu ya wuce sanarwar gargadi ta yau da kullum; sun mayar da shi kamar ƙidayar lokacin da bala'i zai iya faruwa.
Sai dai Fatima, wadda take magana daga Garissa, ba ta nuna alamun karaya ko fitar da rai ba. Ta ga abin da ke faruwa idan ruwan sama ya sauka kuma aka yi watsi da gargaɗin da aka bayar. Haka kuma, ta ga abin da ke faruwa idan aka ɗauki matakan da suka dace.
"A shekarar 1997, ba mu san komai ba. Amma yanzu mun sani," in ji ta. "Idan gwamnati ta kawo alluran rigakafi da gidan sauro, kuma matasa suka saurari shawarwarin, za mu iya ceton dabbobinmu, mu kuma ceci kanmu. Ruwan sama zai sauka. Amma ba lallai ne mu mutu tare da shi ba."



















