| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Harin kare kan wata 'yar Afirka ta Kudu ya janyo kiraye-kirayen dokoki masu tsauri
Ana neman kare ɗaya yayin da aka kashe karnuka biyu cikin wani yanayi na tausayi.
Harin kare kan wata 'yar Afirka ta Kudu ya janyo kiraye-kirayen dokoki masu tsauri
Waɗanda ke wucewa sun yi yekuwa kuma sun yi ƙoƙarin taimaka, amma Kweleta ta mutu daga baya sakamakon raunin da ta ji

Ƙungiyar masu kiwon kare irin na Pit Bull na Afirka Ta Kudu (PBFSA) tana kira ga hukumomin gwamnati su ƙaddamar da dokokin tsaurara mallakar karnuka masu ƙarfi biyo bayan harin kisan da karnuka suka afka wa wata mai shekara 28 a Montclair, dake kudancin Durban.

Wadda lamarin ya shafa tana tafiya ne a kan hanyar gwamnati a lokacin da karnuka uku masu ƙarfi da ake ce wa pit bull suka afka mata kuma suka kashe ta. An binne ta ne a ƙarshen mako.

Kafafan watsa labaran ƙasar sun ruwaito cewa matar wadda aka bayyana cewa sunanata ne Nomathemba Kweleta tana kan hanyarta ta dawowa ne daga sayan kayan cefane a lokacin da karnukan suka kewata kuma suka far mata.

Waɗanda ke wucewa sun yi yekuwa kuma sun yi ƙoƙarin taimakawa, amma Kweleta ta mutu daga baya sakamakon raunin da ta ji.

Biyo bayan aukuwar lamarin, wani mai gadi ya harbe kare ɗaya kuma daga baya ya kashe shi cikin tausayi a wata cibiya ta hana cin zalin dabbobi.

An kama wani kare na biyu kusa da wurin daga wurin da lamarin ya auku kuma daga baya aka kashe shi cikin tausayi. Kare na ukun dai ana nemansa ruwa a jallo a lokacin rahoton.

Rahoton kafar SABC News ta ƙasar ta ba da rahoton cewa harin ya sake buɗe tattaunawa game da dokokin garuruwa da kuma nauyin da ya kamata masu karnuka suɗauka a lokacin da suka mallaki karnuka masu ƙarfi.

Rashin horaswa

Ƙungiyar PBFSA ta ce lammuran tsaro a bainar jama’a da ke da alaƙa da karnuka masu ƙarfi da rashin keɓe su da kiwonsu ba tare da ƙa’ida ba.

"Ƙarnuka masu ƙarfi, irin su, ba dabbobin gida irin ba na iyalai na yau da kullum ba ne," in ji ƙungiyar, tana mai jaddada cewa waɗannan dabbobin suna buƙatar sa-ido na msamman da kuma ƙwarewa wajen tafiyar da su.

A martani ga kiraye-kirayen da ake samu daga ƙungiyoyin masu fafatuka na neman haramta irin karnukan, in ji mai magana da yawun PBFSA Lehanda Rheeder wadda ta ce ya kamata a ɗabbaka dokar ta mayar da hankali kan fayyace gaskiya na masu karnukan da kuma bincike na doka maimakon haramtawa gaba ɗaya.

Rheeder ta ce "ya kamata a samu ƙa’ida mai tsauri game da waɗanda za su iya mallakar kare pit bull," tana mai kira ga sa-ido na garuruwa domin tantance ko waɗanda ke son mallakar karen suna da inda za su saka su da kuma horaswar da ta dace .

Rumbun Labarai
Shugaban Nijar Tiani ya sauya wasu ministocinsa
Shugabar Majalisar Dokokin Cabo Verde ta zama shugabar ƙasar ta riƙo
Harin ta'addanci ya yi ajalin sojojin Mali aƙalla 50, da sojojin haya na Rasha biyar
Ƙasashen Afirka biyar sun kawar da yaɗuwar cutar shan inna, amma ba a gama yaƙin ba
Nabil Neghiz ya zama kocin tawagar Mena ta Nijar
Fiye da mutum 7,000 sun kamu da annobar Ebola a Jamhuriyar Kongo
Shugaban Nijar ya naɗa Birgediya Janar Mamane Sani Kiaou a matsayin sabon shugaban hafsan sojoji
FIFA ta musanta iƙirarin Maroko na 'karɓar baƙuncin' wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na 2030
Majalisar Sudan ta cire 'yantawayen RSF daga tattaunawar ƙasa
An raba mutane fiye da 4,500 da gidajensu a Darfur ta Kudu da Blue Nile saboda matsalar tsaro
An ceto fiye da 'yan ci-rani 1,000 kusa da tekun yammacin Afirka cikin mako ɗaya, in ji MSF
Shugaban Zambia Hichilema ya yi farin ciki da masoyan da suka ba shi kyautar kazar gida
Gwamnatin Ghana ta kashe $4.37m don kwashe 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu
Gwamnatin Nijar ta yi kira ga jama'a su duƙufa da Al-Ƙunut domin neman tsari daga 'maƙiyan ƙasa'
Kwalara ta kashe mutum 23 a Sudan, fiye da 310 sun kamu da cutar
Majalisar Dinkin Duniya ta amince a sake zana taswirar Afirka zuwa ainihin yadda nahiyar take
Nijar na zargin Faransa da tunzura sojojin da suka yi yunkurin tawayen da aka dakile
Tallafin ƙasashen waje da harin jiragen sama marasa matuƙa sun ƙara tsananta yaƙin Sudan - MDD
Babban hafsan sojin Sudan Burhan na rangaɗi game da shirin yaƙi a fagen yaƙin Blue Nile
Dubban mutane sun yi zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga sojin Nijar bayan dakile yunƙurin tawaye