Shugaban majalisar mulkin Sudan Abdel Fattah al Burhan ya ce "sojin ƙasar sun janye daga Al Fasher", bayan wata sanawar da ke cewa rundunar RSF ta ƙwace birnin.
"Mun yarda mu janye sojoji daga Al Fasher zuwa wani wuri da ya fi tsaro," kamar yadda ya bayyana a jawabin da ya gabatar a kafar talbijin ɗin ƙasar ranar Litinin, yana mai jaddada cewa ɓangarensa "zai ɗauki fansa " kuma ya yi yaƙi "har sai lokacin da aka tsaftace ƙasar ".
Sanarwar ita ce ta farko inda Burhan ya yarda cewa ya rasa Al Fasher bayan rundunar RSF, wadda dakarunta suke yaƙi tun watan Afrilun shekarar 2023, ta yi shelar samun nasara a birnin na yammacin Darfur ranar Lahadi.
Birnin mai muhimmanci ya kasance ƙarƙashin ƙawanyar rundunar tun watan Mayun shekarar 2024.
Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) mai kula da Hijira ta bayyana ranar Litinin cewa fiye da mutum 26,000 ne suka tsere daga yaƙi a Al Fasher tun ranar Lahadi, inda suke neman mafaka a wajen birnin ko kuma suka nufi Tawila, da ke da nisan kilomita 70 yamma da birnin.
MDD ta ce fiye da mutum miliyan ɗaya ne suka tsere daga birnin tun lokacin da aka fara yaƙin yayin da kimanin fararen-hula 260,000—rabinsu ƙananan yara— suka maƙale ba tare da agaji ba inda da yawa daga cikinsu suka koma cin abincin dabbobi.
Ƙwace Al Fasher ya baiwa rundunar RSF iko a kan sama da manyan biranen jihohi biyar a Darfur, lamarin da ya ƙarfafa ikonta a Nyala, babban birnin jihar South Darfur.
A halin yanzu ikon sojin ƙasar ya tsaya ne kawai a arewaci da gabashi da kuma tsakiyar Sudan.










