Tarihin rayuwar marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da gudunmawarsa ga addinin Musulunci
NIJERIYA
2 minti karatu
Tarihin rayuwar marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da gudunmawarsa ga addinin MusulunciMarigayi Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne dab da asubahin Alhamis 27 ga watan Nuwamba bayan gajeriyar jinya, ya bar gado mai yawa na ilimi, mabiya, da tasiri a fagen addini da zamantakewa a Nijeriya.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi / TRT Afrika Hausa
27 Nuwamba 2025

Tafsirinsa ya shahara matuƙa kuma an fi yada shi a rediyo, talabijin, da kuma kafofin sada zumunta.

Ya shahara da yawon wa’azi a jihohi daban-daban na Nijeriya da ƙasashen waje, inda yake mai da hankali kan koyar da tauhidi, shari'a, ɗorewar ɗabi'a masu kyau, da kiran zaman lafiya.

Dangantaka da Shehu Ibrahim Inyass

Dangantakarsa da gidan Shehu Ibrahim Inyas, Senegal, ta ƙara ƙarfafa matsayinsa a matsayin jagoran Tijjaniyya na Afirka ta Yamma. Ya kasance babban almajiri, mabiyi kuma masoyin Shehu Ibrahim Inyas,.

Ya ƙarfafa dangantakar sa da gidan Shehu Inyas, ta hanyar auratayya; ya auri ‘ya’yan Sheikh Ibrahim guda biyu. Ya auri ta biyu ne bayan matarsa ta farko a gidan Shehu Ibrahim Inyas ta rasu.

 
 Tsawon Rai da Iyali

Ya kasance mai tsawon rai, inda ya kai shekara 100 a lissafin kalandar Musulunci, ko kuma shekaru 98 a kalandar Bature. Ya bayyana a cikin wata hira cewa Allah ya hore masa 'ya'ya masu yawa, waɗanda a lokacin ya ce sun kai 90.

Sannan ya ce aƙalla 70 daga cikin ‘ya’yansa sun haddace alƙur’ani, wanda ke nuna yadda Allah ya albarkaci rayuwarsa.

A shekarar 2014, ya tsira daga wani mummunan harin bam da aka kai wa ayarin motocinsa a Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Wannan ya nuna haɗarin da ya fuskanta a kan hanyar da'awarsa.

 An bashi lambar girmamawa ta Officer of the Order of the Federal Republic (OFR) a Najeriya.

Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne dab da asubahin Alhamis 27 ga watan Nuwamba bayan gajeriya jinya, ya bar gado mai yawa na ilimi, mabiya, da tasiri a fagen addini da zamantakewa a Nijeriya.





Rumbun Labarai
'Yanta'adda sun sace fiye da mutum 300 a Jihar Bornon Nijeriya, in ji hukumomi
Ce-ce-ku-ce bayan dakatar da Sheikh Alƙali Zaria daga Tafsirin Ramadan a Nijeriya
An gabatar da kudirin tsige mataimakin gwamnan Kano a gaban majalisar dokokin jihar
'Yanta'addan ISWAP sun kashe sojojin Nijeriya 14 a hare-hare biyu
Tinubu ya ba da umarnin fitar da kudi nan-take don gyara kayan aikin sararin samaniyar Nijeriya
Nijeriya ta tara fiye da naira tiriliyan biyu daga harajin VAT a wata uku na karshen 2025 – NBS
'Yanbindiga sun raba fiye da mutum 300,00 da gidajensu a jihar Neja – Gwamna Bago
Ramadan: INEC ta sauya ranakun zaɓen 2027
An kashe aƙalla mutum 25 a wani hari da ake zargin Boko Haram da kai wa a Jihar Adamawa a Nijeriya
Hare-haren ƙungiyoyin 'yanta'adda kan iyakokin Nijar, Benin da Nijeriya na ƙaruwa: Bincike
Ƙalubalen da ke gaban sabon Sufeto Janar na 'yansandan Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin biyan kudin fansa don ceto daliban Jihar Neja
'Yansandan Nijeriya sun kashe ɓarayin daji tare da kama mai safarar makamai a Kaduna
Tarayyar Afirka ta nemi a 'ɗauki mataki' bayan an kashe gomman mutane a Zamfara a Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda 25 masu alaƙa da Daesh a jihar Borno
NDLEA ta kama matar da ta kifa ƙwarya a matsayin cikin bogi don ɓoye ƙwayoyi
Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta lashe zaɓukan cike gurbin da aka gudanar a Kano
Nijeriya: 'Yanbindiga sun kashe mutum 50 da garkuwa da wasu da dama a Jihar Zamfara
Hukumar NCDC ta Nijeriya ta tabbatar da samun mutum 318 ɗauke da zazzaɓin Lassa da mutuwar mutum 70
Gobara ta ƙona shaguna aƙalla 50 a Kasuwar Fatima Simra a Kanon Nijeriya