Tarihin rayuwar marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da gudunmawarsa ga addinin Musulunci
Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne dab da asubahin Alhamis 27 ga watan Nuwamba bayan gajeriyar jinya, ya bar gado mai yawa na ilimi, mabiya, da tasiri a fagen addini da zamantakewa a Nijeriya.
Tafsirinsa ya shahara matuƙa kuma an fi yada shi a rediyo, talabijin, da kuma kafofin sada zumunta.
Ya shahara da yawon wa’azi a jihohi daban-daban na Nijeriya da ƙasashen waje, inda yake mai da hankali kan koyar da tauhidi, shari'a, ɗorewar ɗabi'a masu kyau, da kiran zaman lafiya.
Dangantaka da Shehu Ibrahim Inyass
Dangantakarsa da gidan Shehu Ibrahim Inyas, Senegal, ta ƙara ƙarfafa matsayinsa a matsayin jagoran Tijjaniyya na Afirka ta Yamma. Ya kasance babban almajiri, mabiyi kuma masoyin Shehu Ibrahim Inyas,.
Ya ƙarfafa dangantakar sa da gidan Shehu Inyas, ta hanyar auratayya; ya auri ‘ya’yan Sheikh Ibrahim guda biyu. Ya auri ta biyu ne bayan matarsa ta farko a gidan Shehu Ibrahim Inyas ta rasu.
Tsawon Rai da Iyali
Ya kasance mai tsawon rai, inda ya kai shekara 100 a lissafin kalandar Musulunci, ko kuma shekaru 98 a kalandar Bature. Ya bayyana a cikin wata hira cewa Allah ya hore masa 'ya'ya masu yawa, waɗanda a lokacin ya ce sun kai 90.
Sannan ya ce aƙalla 70 daga cikin ‘ya’yansa sun haddace alƙur’ani, wanda ke nuna yadda Allah ya albarkaci rayuwarsa.
A shekarar 2014, ya tsira daga wani mummunan harin bam da aka kai wa ayarin motocinsa a Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Wannan ya nuna haɗarin da ya fuskanta a kan hanyar da'awarsa.
An bashi lambar girmamawa ta Officer of the Order of the Federal Republic (OFR) a Najeriya.
Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne dab da asubahin Alhamis 27 ga watan Nuwamba bayan gajeriya jinya, ya bar gado mai yawa na ilimi, mabiya, da tasiri a fagen addini da zamantakewa a Nijeriya.