| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yansandan Nijeriya sun fara bincike kan kashe wata mata da 'ya'yanta shida a Kano
Rundunar 'yansandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta tabbatar da kisan wata mata mai suna Fatima Abubakar da 'ya'yanta shida a a unguwar Dorayi Charanchi da ke cikin birnin Kano
'Yansandan Nijeriya sun fara bincike kan kashe wata mata da 'ya'yanta shida a Kano
‘Yansandan sun ce a yayin harin, ana zargin maharan da amfani da muggan makamai wurin aikata wannan ta’asar. / Abdullahi Haruna Kiyawa
17 Janairu 2026

Rundunar ’Yansandan Nijeriya Reshen Jihar Kano ta kaddamar da bincike kan wani mummunan hari da aka kai wa wata mata da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Charanchi da ke cikin birnin Kano, lamarin da ya yi sanadin mutuwar matar da ‘ya’yan nata.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:10 na rana a ranar 17 ga Janairun 2025, lokacin da ’yan sanda suka karɓi kiran gaggawa da ke nuna cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidan Haruna Bashir a unguwar Dorayi Charanchi.

‘Yansandan sun ce a yayin harin, ana zargin maharan da amfani da muggan makamai wurin aikata wannan ta’asar.

Rundunar ‘yansandan ta ce mahaifiyar yaran da aka kashe sunanta Fatima Abubakar mai shekara 35. Sun samu munanan raunuka a yayin harin, kuma an garzaya da su zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.

Bayan samun rahoton, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya gaggauta tura tawagar ’yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, kamar yadda sanarwar da ‘yansandan suka fitar ta bayyana.

Tawagar ta kasance karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Ayyuka, DCP Lawal Isah Mani, domin tabbatar da tsaron yankin da kuma fara binciken farko.

Kwamishinan ’Yan Sandan ya kuma umarci Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID), ACP Wada Jarma, da ya jagoranci cikakken bincike domin ganowa tare da kama waɗanda ke da hannu a harin.

 

Rumbun Labarai
Jan hankalin gwamnatin Nijeriya ga 'yan ƙasar masu shiga yaƙi a wasu ƙasashen ƙetare
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta daƙile hare-haren 'yan ta'adda a jihar Borno
Nijeriya ta gargaɗi ‘yan ƙasar kan faɗawa tarkon masu ɗaukar ma’aikata su tura su wurin yaƙi
'Yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 30 a Jihar Neja ta Nijeriya, sun ƙona ofishin 'yansanda
'Yanbindiga sun kashe DPO na 'yansandan Nijeriya a Jihar Katsina
'Rashin sake wa hukumomin gwamnatin Nijeriya kuɗaɗen kasafi koma-baya ne ga ci gaban ƙasa'
Za a yi zaben Shugaban Kasa a Nijeriya ranar 20 ga Fabrairun 2027, in ji INEC
Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Nijeriya ta kori ma'aikatanta 43 kan saɓa wa dokar aiki
Jami'an tsaro sun ƙwace fasfon Nasir El-Rufa'i bayan yunkurin kama shi ya ci tura a filin jirgi
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yan Boko Haram 16 a Borno
CBN ya bai wa 'yan canji a Nijeriya damar sayen dala 150,000 a duk mako daga gwamnati
Amurka za ta tura sojojinta 200 Nijeriya
Sojojin Nijeriya sun kashe gomman 'yan-ta'adda, sun dawo da mutum 700 gida a arewa maso gabas
Me ya sa Kannywood ke fafutuka yayin da Nollywood ke samun tagomashi?
Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ya ajiye aikinsa
Mutum fiye da 30 sun rasu sakamakon hatsarin mota a Jihar Kano
Nijeriya: 'Yanbindiga sun sace wani faston Katolika a Kaduna, sun kashe mutum uku
Nijeriya da Nijar sun ƙulla yarjejeniya kan jigilar kayayyaki da tsaron kan iyaka
Shugaba Tinubu na Nijeriya na shirin kai ziyarar aiki London a watan Maris
Jerin hare-hare sun yi sanadin mutuwar mutum 30 a Jihar Benue ta Nijeriya