Burhan na Sudan ya yi watsi da yarjejeniya ya ce za a cim ma tsagaita wuta ne bayan janyewar tsageru
Abdel Fattah al-Burhan ya ce kamata y yi wadanda ke kiran gwamnati da ta bayar da kai bori ya hau, su yi kira ga ‘yan tawaye da su mika wuya.
Shugaban Majalisar Mulkin Sojin Sudan Abdel Fattah al Burhan ya yi watsi da duk wata yarjejeniya ko tsagaita wuta da mayakan 'yan tawaye, muddin suka ci gaba da zama a yankin Sudan, yana mai cewa zaman lafiya zai iya biyo bayan dawo da cikakken ikon gwamnati, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan.
"Sudan ba za ta amince da tsagaita yarjejeniya ko tsagaita wuta ba muddin 'yan tawayen suka ci gaba da kasancewa a kowane bangare na kasar," in ji al-Burhan.
Ya yi wannan jawabin ne a lokacin wani taro da ya yi da shugabannin al'ummar Sudan da Turkiyya, wakilan kungiyoyin farar hula, da kuma manyan 'yan jarida a ofishin jakadancin Sudan da ke Ankara a ranar Lahadi, 28 ga Disamba.
Al Burhan ya ce shirin zaman lafiya da Firaminista Kamil Idris ya gabatar a Majalisar Dinkin Duniya da ke New York yana wakiltar hangen nesa na gwamnati guda daya don kawo karshen rikicin.
Ya bayyana cewa Majalisar Mulkin Sojin da Majalisar Ministoci sun amince da shirin, tare da shirya karin tattaunawa a cikin Majalisar Tsaro don tabbatar da an amince da shi a fadin cibiyoyin gwamnati..
‘Ba masu son a yi yaki ba ce’
"Wannan wani shiri ne na Gwamnatin Sudan," in ji shi, yana mai bayyana shi a matsayin "shirin da shi kadai ne zai iya cim ma burin al'ummar Sudan."
Duk da matsayinsa, al Burhan ya jaddada cewa gwamnati ba ta neman dogon rikici. "Ba masu goyon bayan yaki ba ne mu," in ji shi.
Ya sake nanata amincewarsa ga Sojojin Sudan kuma ya yi kira ga wadanda a baya suka bukaci yin sulhu da mayaka 'yan bindiga da su sauya sakonsu. "Waɗanda suka kira mu bayar da kai bori ya hau su fara shawartar 'yan bindigar da su mika wuya," in ji shi.
Da ya juya zuwa ga yanayin yankin, al Burhan ya ce Sudan ta amince da manufofin Saudiyya da Masar kuma ta yi imanin cewa kasashen biyu za su iya taka rawa mai kyau wajen warware rikicin da kuma ci gaba da zaman lafiya a nan gaba.
‘Ba kasa mai kai harin zalunci ce’
"Sudan ba ta taɓa zama mai kai hari ga kowace ƙasa maƙwabciyarta ba," in ji shi, yayin da yake amincewa da tasirin yaƙin a yankin. "Mun san da tarin sojoji a nan da can, kuma Sudan ba ƙasa ce mai rauni ba." Ya ƙara da cewa Khartoum tana da 'yancin kare kanta.
Al Burhan ya kuma yaba da dangantaka 'ta tarihi, ta 'yan'uwantaka' da suke da ita da Turkiyya, yana mai bayyana dangantakar Sudan da Turkiyya a matsayin shiga cikin "haɗin gwiwa mai kyau da hangen nesa".
A ranar Alhamis da ta gabata, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Abdel Fattah al Burhan sun tattauna dangantakar ƙasashen biyu da kuma ci gaban yanki da na duniya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Ankara.