Man fetur yana tsada sosai, amma mu gode wa Allah halin da muke ciki ya fi na wasu ƙasashe – Tinubu
Tinubu ya kwatanta halin da Nijeriya ke ciki da na sauran ƙasashen Afirka, inda ya bayyana cewa wannan ƙalubalen ba a ƙasarsa kaɗai ya tsaya ba.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce ya san irin wahalhalun da ake fuskanta sakamakon hauhawar farashin man fetur, inda ya buƙaci ’yan ƙasar da su ci gaba da kasancewa masu nuna ƙarfin hali, yana mai cewa har yanzu ƙasar tana cikin yanayi mai kyau idan aka kwatanta da wasu ƙasashe.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Jumma’a yayin ziyarar da ya kai jihar Bayelsa, inda ya ƙaddamar da wasu ayyuka.
Yayin da yake tsokaci kan damuwar da ake nunawa game da taɓarɓarewar tattalin arzikin Nijeriya, Tinubu ya ce, “Ina jin koke-kokenku daga fannoni daban-daban na tattalin arziki. Farashin man fetur ya yi tsada sosai, amma ku duba wasu ƙasashe, kawai mu gode wa Allah tare cewa halin da kuke ciki ya fi na wasu kyawu.”
Tinubu ya kwatanta halin da Nijeriya ke ciki da na sauran ƙasashen Afirka, inda ya bayyana cewa wannan ƙalubalen ba a nan kaɗai ya tsaya ba.
“Ku duba abin da ke faruwa a Kenya, da ma sauran ƙasashen Afirka, ku ji irin abubuwan da suke fuskanta. Ba za mu koma baya ba. Za mu ci gaba da nemo hanyoyin rage raɗaɗin wahala ga marasa ƙarfi. Wannan gwamnati ce mai nuna kulawa,” in ji shi.
Shugaban ya ce gwamnati na ƙoƙarin sauƙaƙa wa ’yan ƙasa matsalolin da suke fuskanta, sannan ya ɗora alhakin matsin tattalin arzikin kan wasu abubuwa da suka shafi duniya baki ɗaya.
“Na yi farin cikin cewa Shugaban Ma’aikata yana nan. Dubi alƙaluman da ke tattare da harkar kuɗi, tsare-tsaren tattalin arziki, da kasafi, kuma za mu ga abin da za mu iya yi don sauƙaƙa wannan nauyi.
“Amma wannan shi ne ci-gaban; nauyin hakan shi ne abin da muke fuskanta a yau. Ƙalubalen yaƙin da ba mu ne muka jawo shi ba, amma sakamakon yadda duniya take a dunƙule wuri guda. Daɗi da rashinsa duk abu ne da yake shafar duniya gaba ɗaya,” in ji shi.
Tun bayan hawan mulkinsa a watan Mayun 2023, gwamnatin Tinubu ta aiwatar da jerin garambawul a fannin tattalin arziki, waɗanda suka haɗa da janye tallafin man fetur da kuma barin naira ta nemar wa kanta daraja a kasuwa.
Duk da cewa waɗannan ƙudurori na nufin tabbatar da daidaiton tattalin arziki na dogon lokaci, sun haifar da ƙaruwar matsi ga ’yan ƙasar da dama, sakamakon tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki da kuma tsadar rayuwa.